Idan kunne ya ji: Daga zuwa kwanan gida an tsini gawar wata budurwa a dakin saurayinta

Idan kunne ya ji: Daga zuwa kwanan gida an tsini gawar wata budurwa a dakin saurayinta

Wata babbar kotun majistri dake zamanta a unguwar Iyaganku cikin babban birnin jahar Oyo, Ibadan ta bada umarnin garkame wani mutumi mai suna Olaosebikan Sangodiji a gidan kurkukun Agodi bayan akan tuhumar kisan kai da ake yi masa.

An gurfanar da Sangodiji mai shekaru 44 gaban kotun majistri ne sakamakon tuhumar kisan kai da ake yi masa, inda ake zarginsa ya kashe budurwarsa mai suna Dupe Oluwole, yar shekara 26 a dakinsa dake unguwar Sangodiji, Asapopo cikin yanki Illaro na jahar Oyo.

KU KARANTA: Gobara ta lakume wani dan jariri mai watanni 3 a Duniya kacal a Kano

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dansanda mai shigar da kara, Sajan Segun Adegboye ya bayyana ma kotu cewa da misalin karfe 8 na safiyar ranar 12 ga watan Disambar shekarar 2018 ne Sangodiji ya murde wuyan budurwarsa, Dupe.

“Muna zargin wanda ake kara yana soyayya da mamaciyar ne, wanda hakan yasa ya gayyaceta zuwa dakinsa, amma tashin da aka yi washe gari sai aka tsinci gawarta a gidansa. Hakan ya saba ma sashi na 316 na kundin hukunta manyan laifuka na jahar Oyo” inji Dansanda.

Sai dai wani lauya mai zaman kansa, Adewale Mosadomi ya bayyana a gaban kotu da nufin kare wanda ake kara, amma kotun bata gamsu ba, inda Alkalin kotun, E. Idowu ya bayyana cewa kotun bata da hurumin sauraron karar.

Don haka Alkali Idowu ya mika shari’ar zuwa ofishin babban jami’I mai shigar da kara na jahar Oyo domin samun shawarar kwararru, daga karshe kuma y adage sauraron karar zuwa ranar 6 ga watan Maris na shekarar 2019.

A wani labarin kuma, shahararren marubucin nan, Farfesa Wole Soyinka ya nuna yatsa ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da mataimakinsa, Atiku Abuabakar game da kisan tsohon ministan sharia kuma babban kauyan gwamnati a zamanin mulkinsu, Cif Bola Ige.

Soyinka ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Laraba, 6, ga watan Feburairu, inda ya tuna ma Duniya cewa a shekarar 2001 aka kashe Bola Ige, kimanin shekaru biyu kenan bayan nada shi Ministan sharia.

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel