Matar aure ta mutu a dakin saurayinta bayan ta gama cin amanar mijinta
Hukumar 'yan sanda na jihar Ogun ta damke wani saurayi dan shekaru 28 saboda rasuwar wata matan aure mai shekaru 40 da tace ga garinku bayan sun gama saduwa da saurayin.
Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, Abimbola Oyeyemi, ya ce an damke wanda ake zargin ne a ranar Laraba bayan asibti ta shigar da kara a caji Ofis.
Ya ce wanda ake zargin ya kai gawar marigayiyar asibiti jihar ta Ota kuma baiyi bayanin dalilin rasuwarta ba.
"An damke wanda ake zargin ne bayan wani Benjamin Okereke dake asibitin jiha ta Ota ya janyi hankalin asibitin cewa wanda ya kawo gawar marigayiyar ya kasa yiwa asibitin bayanin abinda ya yi sanadin rasuwarta," inji shi.
DUBA WANNAN: Takkadama: Kan Sanatocin APC ya rabu a kan maye gurbin Saraki
Mr Oyeyemi yace bayan sun sami rahoton, DPO na caji ofis din Onipanu, Sangobiyi Johnson, ya jagoranci 'yan sanda zuwa asibitin inda suka kama wanda ake zargin nan take.
Bayan kama shi, wanda ake zargin ya shaidawa 'yan sanda cewa ya hadu da marigayiyan a cikin bus a Ketu kuma su kayi musayar lamaban waya, daga baya ya gayyace ta gidan abokinsa inda suka tara amma bayan sun gama sai ta yanke jiki ta mutu.
A yayin da aka tuntubi mijin matan, Idowu Lamidi, direban mota ya shaidawa yan sanda cewa matarsa ta bar gida cikin koshin lafiya domin zuwa wajen aiki kuma yana mamakin abinda ya yi sanadin rasuwarta.
Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Ahmed Iliyasu ya bayar da umurnin a cigaba da binciken a sashin binciken masu aikata manyan laifuka domin gano musababin abinda ya yi sanadiyar rasuwar matar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng