Sanata Ndume Ya ‘Gano’ Makircin Masu Kiran a Kori Hafsoshin Tsaro, Ya Gargadi Tinubu
- Sanatan Borno ta Kudu, Mohammad Ali Ndume ya yi martani game da rokon da ake yi wa shugaban kasa ya kori hafsoshin tsaro
- Ndume ya roƙi Shugaba Bola Tinubu da ka da ya saurari masu kira da a tsige hafsoshin tsaro, yana cewa hakan zai rage kwarin gwiwa
- Kungiyar Northern Ethnic Nationalities Forum ta nemi cire shugabbannin tsaro, tana zargin rashin iya aiki duk da kuɗin da ake warewa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Sanata Ali Ndume ya bayyana matsayarsa kan masu neman a kori hafsoshin tsaro a Najeriya saboda halin da ake ciki.
Ndume ya roƙi Shugaba Bola Tinubu da ka da ya saurari kiraye-kirayen tsige hafsoshin tsaro saboda illar hakan ga sojoji.

Source: Facebook
Sanata Ndume wanda ke wakiltar mazabar Borno ta Kudu ya yi wannan kira ne a cikin wata sanarwa da Punch ta samu a yau Alhamis 11 ga watan Satumbar 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An roki Tinubu ya kori shugabannin tsaro
Hakan na zuwa ne bayan kiraye-kirayen wasu da ke neman shugaban kasa, Bola Tinubu domin ya kori shugabannin tsaro a kasar.
Kungiyar 'Northern Ethnic Nationalities Forum' na daga cikin wadanda suka yi ta kiran a sallami hafsoshin tsaro.
Kungiyar ta ce:
“Cikin bacin rai muna kiran da a yi gaggawar sallamar shugabannin hukumomin tsaro da kuma sauya su da wasu nan take."

Source: Twitter
Tsaro: Ndume ya caccaki masu shawartar Tinubu
Sai dai Sanata Ndume ya ce duk masu neman a sallami shugabannin tsaron suna da wata manufa ta daban a zuciyarsu, Vanguard ta ruwaito.
Ndume ya ce:
“Duk wadanda ke kiran a kori hafsoshin tsaro a Najeriya suna da wata manufa ta daban a cikin zuciyarsu kuma babu alheri tare da su.
“Shiririta ce da rashin sanin ya kamata wata kungiya ta zargi shugabannin tsaro da rashin katabus kan aikinsu."
Shawarar Ndume ga hukumomi kan tsaro
Sanatan ya yi kira da a maida hankali kan horaswa da ba da kayan aiki da kuma karfafa guiwar jami'an tsaro domin karfafa dakarun da yaki da ta’addanci.
Ya ƙara da cewa:
“Abin da fa kawai suke bukata yanzu shi ne kayan aiki da kuma karfafa musu guiwa, albashin soja ya kai N100,000.
“Ya kamata mutane su guji maganganu da zai iya rage kwarin guiwar da jami'an tsaro da kuma wadanda suke bakin daga."
Sanatan ya ce abin da ya fi dacewa shi ne karfafa sojoji da kayan zamani fiye da sauya shugabanci, tare da yabon Shugaba Tinubu bisa kawo sauyi.
2027: Ndume ya nesanta kansa da Tinubu
Mun ba ku labarin cewa Sanata Ali Ndume ya nesanta kansa daga goyon bayan Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sake tsayawa takara a babban zaben 2027.
Ndume ya bayyana haka ne bayan matsayar gwamnonin APC 22 na goyon bayan Shugaba Tinubu a matsayin dan takararsu a zabe mai zuwa.
Sanatan ya ce halin da kasa ke ciki a yanzu, jama'a suna cikin mawuyacin halin da bai dace a rika maganar sake takarar Tinubu ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

