Mele Kyari: Yadda Ta Kaya bayan EFCC Ta Titsiye Tsohon Shugaban Kamfanin NNPCL

Mele Kyari: Yadda Ta Kaya bayan EFCC Ta Titsiye Tsohon Shugaban Kamfanin NNPCL

  • Hukumar EFCC ta yi wa tsohon shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari, tambayoyi kan zargin karkatar da dala biliyan 7.2
  • An ware kudin ne domin gyaran matatun mai mallakin gwamnati da ke Port Harcourt, Warri da Kaduna a lokacin da yake ofis
  • Har zuwa daren ranar Laraba, Mele Kyari yana karkashin bincike a hedkwatar hukumar EFCC da ke Abuja

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja – Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta yi wa tsohon shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Mele Kyari, tambayoyi.

Hukumar EFCC ta titsiye Mele Kyari ne kan zargin karkatar da kudin gyaran matatun mai da su ka kai Dala biliyan 7.2.

Mele Kyari ya sha tambayoyi a hannun EFCC
Hoton tsohon shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari da shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede Hoto: @nnpclimited, @OfficialEFCC
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa tsohon shugaban kamfanin na NNPCL, ya hadu da jami'an hukumar EFCC ne a ranar Laraba, 10 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta gurfanar da 'yar takarar PDP a kotu kan zargin sabawa doka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan Mele Kyari ya je hedkwatar EFCC, an kai shi daki na musamman, inda aka fara yi masa tambayoyi.

EFCC na binciken kudin gyaran matatun NNPCL

Majiyoyi daga hukumar EFCC sun bayyana cewa an gayyaci Mele Kyari ne domin ya fayyace yadda aka gudanar da wasu harkokin kudi a lokacin da yake jagorantar kamfanin NNPCL.

Vanguard ta tababtar da cewa daya daga cikin majiyoyin, ya bayyana cewa an gayyaci Mele Kyari ne musamman don ya ba da bayanai kan kudaden da aka ware don gyaran matatu.

Akwai matatun mai na gwamnati da ke Kaduna, Port Harcourt da Warri.

"Eh, yana ofishinmu. An gayyace shi domin ya yi bayanin yadda aka yi amfani da kudaden da aka ware don gyaran matatun man kasar nan. Wannan ne kawai abin da na sani a yanzu.”

- Wata majiya

Ya kara da cewa saboda tarin takardun da suka shafi binciken, tambayoyin na daukar lokaci, kuma idan jami’an sun gamsu da bayanansa, ana iya ba shi beli na wucin gadi, amma ba a ranar Laraba din ba.

Kara karanta wannan

Mele Kyari: Tsohon shugaban NNPCL ya fada komar EFCC, an ji dalili

Ba a samu jin ta bakin EFCC ba

Kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale, bai daga kiran waya ba kuma bai amsa sakonnin kar-ta-kwana da na WhatsApp da aka tura masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

EFCC ta titsiye Mele Kyari da tambayoyi
Hoton shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari, yana jawabi Hoto: @nnpclimited
Source: Facebook

A lokacin da Kyari ke jagorantar kamfanin NNPCL, an sake gyara wasu matatun mai tare da kaddamar da su.

Sai dai, daga bisani an sake rufe su bayan dan wani lokaci da sanar da cigaban da ake ta murnar an samu a kasar.

Mele Kyari dai ya bar Najeriya bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sauke shi daga shugabancin kamfanin NNPCL.

Babu tabbaci kan lokacin da tsohon shugaban na NNPCL ya dawo gida Najeriya kafin ya kai kansa ga hukumar EFCC.

Ana neman ganin bayan shugabannin NNPCL

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Bashir Bayo Ojulari, ya yi zargin cewa ana yi wa rayuwarsa barazana.

Bayo Ojulari ya bayyana cewa ana harin rayuwarsa ne da sauran shugabannin kamfanin kan sauye-sauyen da ya kawo.

Kara karanta wannan

Hukumar INEC ta raba gardama, ta saki sunayen shugabannin jam'iyyar hadaka, ADC

Ya bayyana cewa ya fara aiwatar da sauye-sauyen ne bisa umarnin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ba shi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng