An Dura kan Bashir Ahmad game da Sukar Kiran Zanga Zanga a Najeriya Kamar Nepal
- Tsohon hadimin Muhammadu Buhari ya sha suka daga ’yan Najeriya bayan ya caccaki masu kiran yin zanga-zanga irin ta Nepal
- Bashir Ahmad ya bayyana cewa “marasa kunya” ne ke son kawo tarzomar a Najeriya, yana mai cewa hakan ba zai kawo alheri ba
- Wannan martani nasa ya fusata mutane da dama, inda wasu ke cewa da shi za su fara idan aka yi irin wannan zanga-zangar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Yan Najeriya da dama sun yi rubdugu kan tsohon hadimin marigayi Muhammadu Buhari kan zanga-zanga a Nepal.
Bashir Ahmad ya sha suka bayan caccakar wasu da ke kiran a gwada zanga-zanga irin yadda aka yi a kasar Nepal a Najeriya.

Source: Twitter
Tsohon hadimin Buhari ya sha sukar bayan wallafa rubutu a shafinsa na X a yau Laraba 10 ga watan Satumbar 2025 da muke ciki.

Kara karanta wannan
Lamari ya kazanta: Masu zanga zanga sun kona matar tsohon Firayim minista a Nepal
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da ke faruwa a kasar Nepal
Hakan ya biyo biyo bayan barkewar zanga-zanga a kasar Nepal wanda ake yi domin nuna bacin rai game da cin hanci da rashawa.
Gungun matasa da suke yin zanga-zangar yaki da rashawa sun tilasta wa Firayim Minista a Nepal, K.P. Sharma Oli yin murabus.
Rikicin ya tsananta a Nepal bayan kashe masu zanga zanga 19 da jikkata sama da 100 sakamakon harbe-harbe da ake zargin ‘yan sanda da yi.
An gano yadda aka cinna wa majalisar dokokin kasar wuta, sannan aka farmaki gidajen ministoci yayin da wasu daga cikinsu suka yi murabus.

Source: Twitter
Nepal: Bashir ya soki masu kiran zanga-zanga
Bashir Ahmad ya gamu da fushin yan Najeriya ne bayan ya soki masu neman a yi zanga-zanga irin ta Nepal a Najeriya.
A cikin rubutunsa, Bashir ya ce rashin kunya ne tsantsa mutum ya rika yi wa kasar Najeriya fatan zanga-zanga irin ta Nepal.

Kara karanta wannan
'Duk da fara shirin sulhu, 'Yan bindiga sun yi kisa, an sace mutane masu yawa a Katsina
Ya ce:
"Marasa kunya da ke neman zanga-zanga irin ta “Nepal” a Najeriya, ba su da wata manufa ta alheri ga ƙasar."
Wannan rubutu da ya yi, ya fusata mutane inda suke ta caccakarsa har wasu na cewa da shi za su fara idan aka zo.
Mafi yawan wadanda suka yi martani sun caccake shi da cewa shi din har wani alherin yake so ga Najeriya?
@muhaisin3:
"Ai har da kai za mu hada idan na mu ya taso, Lol."
@KhingSZN:
"Munafiki."
@addel_cares:
"Su ma yan siyasa da ke sata suna nufin alheri ga Najeriya ko?, mutanen da suke marawa yan bindiga baya a Arewa suna nufin alheri ga Najeriya ko?"
Yan zanga-zanga sun kona matar tsohon firayim minista
Kun ji cewa wasu matasa da ke zanga-zanga a Nepal sun ci gaba da barna bayan Fira ministan kasar ya yi murabus saboda yadda aka taso shi a gaba.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa masu zanga-zangar sun ƙona gidan tsohon Fira minista Jhalanath Khanal, inda matarsa Rabi Laxmi Chitrakar ta ke ciki.

Kara karanta wannan
Matasa sun bankawa majalisa wuta, an tilastawa Firayim Minista yin murabus a Nepal
An ce matar ta rasu sakamakon gobarar da ta tashi wanda aka kai ta asibiti kafin likita ta tabbatar da mutuwarta nan take.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng