Mahajjacin Kano Ya Bata a Lokacin Aikin Hajjin 2025 a Saudiyya, Gwamna Abba Ya Yi Magana
- Daya daga cikin alhazan Kano, Sani Danmaliki daga karamar hukumar Kumbotso ya bata lokacin aikin hajjin bana a kasar Saudiyya
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa na aiki kafada da kafada da hukumomin Saudiyya domin gano mahajjacin
- Amirul Hajji na Kano a wannan shekara kuma Sarkin Karaye, Alhaji Muhammadu Maharaz ya mika rahotonsa ga Gwamna Abba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da cewa daya daga cikin mahajjatan jihar ya bata a kasar Saudiyya yayin aikin hajjin 2025.
Gwamna Abba ya ce gwamnatinsa da Saudiyya na aiki kafada da kafada wajen gano mahajjacin tare da dawo da shi gida cikin iyalansa.

Source: Facebook
Abba Kabir ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi rahoton aikin Hajjin 2025 daga Amirul hajj na Kano, Sarkin Karaye, Alhaji Muhammadu Maharaz, Vanguard ta rahoto.
Gwamnan ya bayyana sunana mahajjacin da ya bace da, Sani Danmaliki daga ƙaramar hukumar Kumbotso.
Abba ya sha alwashin gano mahajjacin
Ya ce gwamnati ta haɗa kai da hukumomin Saudiyya da kuma Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) domin yin duk mai yiyuwa wajen gano inda yake da kuma dawo da shi gida.
Gwamna Abba ya ce:
"A madadin gwamnatin Jihar Kano, ina mika jaje ga iyalan alhajin da ya bace daga Kumbotso.
"Ina kuma tabbatar musu cewa gwamnati tare da hukumomin Saudiyya na ci gaba da yin duk abin da zai yiwu domin gano inda yake.
"Muna fatan Allah ya sa yana raye, kuma in sha Allah zai koma cikin iyalansa. Idan kuwa ya riga mu gidan gaskiya, muna roƙon Allah Ya jikansa Ya kuma ba shi gidan Aljanna.”
Haka kuma, gwamnan ya mika ta’aziyyar gwamnati ga iyalan wasu maniyyata biyu daga jihar da suka rasu a lokacin aikin hajjin na bana.
Gwamna Abba ya yabawa Sarkin Karaye
Ya yaba wa Sarkin Karaye, Alhaji Muhammadu Maharaz, bisa jajircewa da ƙoƙarin da ya yi wajen tabbatar da nasarar aikin hajjin mahajjatan Jihar Kano a bana.
Gwamnan Abba ya gode wa hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kano da ma’aikatanta bisa gudanar da aikin hajji cikin nasara, tare da yin alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa masu.

Source: Facebook
Amirul hajj na Kano ya mika rahoton aikin hajji
A nasa jawabin, shugaban tawagar alhazan Kano kuma Sarkin Karaye, ya bayyana aikin hajjin bana a matsayin ɗaya daga cikin mafi nasara a tarihi.
Ya danganta hakan ne da goyon bayan gwamna, jajircewa da hadin mahajjata da kuma namijin ƙoƙarin hukumar jin daɗin alhazai ta jihar Kano, in ji rahoton Gaurdian.
Ya ƙara da cewa rahoton da aka gabatar, wanda ya ƙunshi nasarori da ƙalubalen da aka fuskanta, zai zama darasi domin ci gaba ga shirye-shiryen aikin hajji na gaba.

Kara karanta wannan
"Mun gano tushen matsalar": Gwamna Uba Sani ya fadi dalilin sulhu da 'yan bindiga
Jami'an Saudiyya sun cafke 'yar Kano a Jeddah
A wani labarin, kun ji cewa jami'an tsaro sun kama wata yar jihar Kano, Maryam Hussaini Abdullahi, yayin da ta je yin Umrah a kasar Saudiyya.
Rahotanni sun nuna cewa an kama Maryam ne bayan da aka danganta sunanta da wata jaka cike da tabar wiwi a filin jirgin sama na Jeddah.
Maryam ta je ƙasar Saudiyya tare da mijinta, Abdullahi Baffa, a ranar 6 ga watan Agusta domin yin Umrah, amma kuma ta fada wannan tarkon.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
