Wata Sabuwa: Gwamnatin Tinubu Za Ta Gyara Dokar Yunkurin Hallaka Kai a Najeriya
- Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da shirin soke laifin yunƙurin kashe kai da ake samu a Najeriya nan da watan Disamba 2025, don rage tsangwama
- Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Pate, ya ce gwamnati ta kafa kwamiti tun 2024 domin jagorantar sauya doka daga daukar hukunci
- An shirya gabatar da kudirin dokar majalisa kan cire laifin yunƙurin kashe kai, domin bin ingantattun hanyoyin kiwon lafiya da rage kisan kai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada kudurinta na kawo sauye-sauye a bangarori da dama domin saukakawa yan kasa.
Gwamnatin Tinubu ta ce za ta cire laifin yunƙurin kashe kai a Najeriya, tare da sanya watan Disamba 2025 a matsayin wa’adin aiwatar da gyaran.

Source: Facebook
Ana neman sauya dokar hallaka kai a Najeriya
Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Pate, ya bayyana haka a taron manema labarai a Abuja, yayin bikin ranar hana kashe kai ta duniya, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan
Majalisa na barazanar hada minista da Tinubu kan 'raina' 'yan Najeriya da suka yi hadari
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, sama da mutum 720,000 ke mutuwa sanadiyyar kashe kai kowace shekara, mafi yawansu daga ƙasashe masu tasowa.
A Najeriya, babban shinge ga neman taimako shi ne sanya yunƙurin kashe kai cikin kundin laifi, abin da ya ƙara tsangwama da tozarta masu rauni daga cikinsu.
Don magance wannan matsalar, gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin kasa a ranar 10 ga Oktoba 2024, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Cheluchi Onyemelukwe.
Pate, wanda babbar sakatariyar ma'aikatar, Daju Kachollom ta wakilta, ya ce:
“An tabbatar da cewa idan an ƙara wayar da kai da kulawa, kisan kai zai ragu sosai, Taken bana shi ne kira da mu maye gurbin rashin magana da tattaunawa, kunya da tausayi, sannan mu gane kalmominmu suna da tasiri.”

Source: Facebook
Hallaka kai: Kokarin gwamnatin Tinubu kan lamarin
Ali Pate ya ce gwamnati ta riga ta fitar da takardar manufofi, tare da kammala kudirin dokar gyara kan dokar lafiyar kwakwalwa ta 2021.
“Bayan haka, zan gabatar da takarda a fadar majalisar zartarwa don samar da kudirin dokar cire laifin yunƙurin kashe kai."
- Cewar Farfesa Ali Pate
A nata jawabin, Kachollom ta ce:
“Hakikanin gaskiya shi ne, sanya yunƙurin kashe kai cikin laifi ba ya ceton rai, sai ƙara tsananta matsalar.”
Shugaban shirin lafiyar kwakwalwa ta ƙasa, Dr. Tunde Ojo, ya ce gyaran ya dace da tsarin duniya inda ake ɗaukar kashe kai a matsayin matsalar lafiya.
A sakonta kan lamarin, Daraktar CHAI a Najeriya, Dr. Olufunke Fasawe, ta ce Najeriya tana matsayi na bakwai a duniya kan yawan kashe kai.
Gwamnatin Tinubu ta magantu kan harajin fetur
Mun ba ku labarin cewa batun sabon haraji kan fetur ya jawo 'yan Najeriya da dama na sukar gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Ministan tattalin arziki, ya fito ya yi magana kan lokacin da za a fara aiwatar da harajin wanda zai sanya a samu karin N45 kan kowace lita.
Wale Edun ya bayyana cewa harajin tsohon abu ne wanda ba gwamnatin Tinubu ba ce ta kirkiro da shi ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
