Da Gaske An Kwace Sarautar da Sarki Ya ba Shugaba Tinubu a Arewa? Gaskiya Ta Fito

Da Gaske An Kwace Sarautar da Sarki Ya ba Shugaba Tinubu a Arewa? Gaskiya Ta Fito

  • Rahoton da ake yadawa cewa an karbe sarautar da aka nadawa Shugaba Bola Tinubu a yankin Idoma ba gaskiya ba ne
  • Majalisar Sarakunan Idoma da ke jihar Benue (IATC) ta ce wasu ne suka kirkiri labarin na karya domin yaudarar jama'a
  • Ta bukaci yan Najeriya musamman kafafen watsa labarai su yi taka-tsantsan, kada su bari a yi amfani da wasu wajen yada karya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Benue - Majalisar Sarakunan Idoma (IATC) ta karyata rahoton cewa ta soke sarautar da Sarkin Adiharu na Igede, Mai Martaba Oga Ero, ya ba Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), George Akume.

A wata sanarwa da sakatare majalisar, Adegbe Uloko, ya fitar, ya bayyana rahotannin da ke yawo a kafafen yada labarai a matsayin "karya da yaudara."

Kara karanta wannan

Cocin katolika ya fusata da zanga zangar adawa da 'ziyarar El Rufa'i' a Imo

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Hoton mai girma shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Abin da ya jawo jitar-jitar kwace sarautar Tinubu

Vanguard ta tattaro cewa a makon da ya gabata ne dai IATC ta sanar da dakatar da bai wa kowa sarauta a yankin Idoma da ke Arewacin Najeriya.

Sai dai a ranar Asabar da ta gabata lokacin bikin Igede Agba, Sarkin Adiharu na Igede ya bai wa wasu mutane sarauta, abin da aka ce ya saba wa wannan umarni.

Wannan ya tayar da ce-ce-ku-ce tsakanin shugabanni da al’umman kabilun Idoma da Igede a yankin Benue ta Kudu da yankin da ke ƙarƙashin IATC.

A cikin sanarwar, IATC ta fayyace cewa babu sunan Tinubu da Sanata Akume a jerin sunayen wadanda aka tsara za a ba sarauta a wurin bikin Igede Agba.

Da gaske an kwace sarautar da aka ba Tinubu?

Majalisar ta ce tun ranar 19 ga watan Agusta, 2025 ta umarci Sarkin Igede, Mai Martaba Oga Ero, da ya dakatar da bai wa kowa sarauta, sannan ta sake jaddada umarnin a hukumance a ranar 2 ga Satumba, 2025.

Kara karanta wannan

Meya sa rubutun Sowore ya fusata DSS? Muhimman abubuwan da ya kamata ku sani

“Tun farko ma babu sunan shugaban kasa ko na Sakataren Gwamnatin Tarayya a cikin jerin wadanda za a karrama da sarauta balle a soke nadin da aka masu.
"Umarnin da aka bayar ya shafi duka sarakunan yankin Idoma, ba Igede kaɗai ba. Don haka labarin cewa an soke sarauta da aka bai wa Tinubu da Akume ba gaskiya ba ne."

Majalisar ta kara da cewa al’amarin na cikin gida ne, kuma tana kokarin magance shi bisa doka ta jihar Benue da kuma al’adun Idoma.

IATC ta gargadi masu yada ƙarya don tada fitina da su daina, tana mai cewa wannan aiki babban laifi ne, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Akume tare da Shugaba Tinubu.
Hoton sakataren gwamnatin tarayya tare da Bola Tinubu a fadar shugaban kasa Hoto: @NGRPresident
Source: Twitter

An gargadi kafafen watsa labarai a Najeriya

Haka kuma majalisar sarakunan ta yi kira ga kafafen yada labarai da su yi taka-tsantsan kada su bari a yi amfani da su wajen bata martabar masarautun gargajiya.

Ta jaddada kudurinta na kare mutuncin masarautar, kiyaye al’adun Idoma, da goyon bayan zaman lafiya da ci gaban jihar Benue da Najeriya baki ɗaya.

An ba Tinubu sarauta a jihar Anambra

A wani rahoton, kun ji cewa sarakunan gargajiya a jihar Anambra sun karrama shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da sarautar, 'Dike si mba Anambra.

Kara karanta wannan

Sawun giwa: Masarauta ta ƙwace sarautar da aka ba Tinubu, ta faɗi manyan dalilai

Sarakunan da suka fito daga sassa daban-daban na jihar Anambra sun ba Tinubu wannan sarauta ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki ta kwana ɗaya.

Shugaban majalisar sarakunan jihar, Eze Chidubem Iweka ya ce sun ba Tinubu sarautar ne saboda kyawawan ayyukan da yake yi a faɗin Najeriya

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262