Tushen Wutar Lantarkin Najeriya Ya Lalace, Al'umma Sun Shiga cikin Duhu a ko ina
- A safiyar ranar Laraba, 10 ga watan Satumba, 2025, tushen wutar lantarki na Najeriya ya sake lalacewa a fadin kasar nan
- Kamfanin rarraba wuta na Abuja (AEDC) ya fitar da sanarwa, da ta tabbatar da katsewar wuta a yankunan da yake kula da su
- An rahoto cewa, karfin wutar lantarki ya ragu zuwa megawatt 50 kacal ga kamfanonin rarraba wutar lantarki na ƙasar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja – Najeriya ta sake fuskantar wani sabon koma-baya a harkar samar da wutar lantarki bayan da tushen wutar lantarki na ƙasar ya durkushe.
Rahotanni sun tabbatar da cewa tushen wutar ya lalace ne da misalin ƙarfe 11:23 na safiyar ranar Laraba, abin da ya jawo katsewar wuta a jihohin ƙasar.

Source: Getty Images
Bayanan da aka tattara daga ISO sun nuna cewa ƙarfin wutar da ake samarwa ya ragu daga 2,917.83MW zuwa 1.5 MW kacal tsakanin ƙarfe 11:00 na safe zuwa 12:00 na rana, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
AEDC ya tabbatar da daukewar wutar lantarki
Wadannan alkaluma sun nuna munin lalacewar wutar wanda ya shafi kusan dukkanin kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos).
Kamfanin rarraba wuta na Abuja (AEDC) ya tabbatar da wannan matsala a cikin sanarwar da ta fitar wa kwastomominta a shafinsa na X.
AEDC ya bayyana cewa rashin wutar lantarki da ake fama da shi a yanzu ya samo asali ne daga lalacewar tushen wutar lantarki na ƙasa.
Sanarwar ta ce:
“Muna sanar da abokan huldarmu cewa, rashin wutar da ake fama da shi a yanzu ya samo asali ne daga tushen wutar lantarki na ƙasa da ya lalace da ƙarfe 11:23 na safe.
"Hakan ya shafi yankunan da muke da alhakin rarraba masu wuta. Muna aiki tare da hukumomi domin dawo da wuta da zarar an gyara wutar daga tushe."
Ƙarancin rarraba wuta a fadin Najeriya
Rahoton The Cable ya nuna cewa da misalin ƙarfe 12:25 na rana, an rarraba jimillar 50 MW kacal ga dukkan kamfanonin rarraba wutar lantarki a faɗin ƙasa.
Ga yadda aka raba wutar:
- Abuja DisCo – 20 MW
- Benin DisCo – 10 MW
- Eko DisCo – 0 MW
- Enugu DisCo – 0 MW
- Ibadan DisCo – 20 MW
- Ikeja DisCo – 0 MW
- Jos DisCo – 0 MW
- Kaduna DisCo – 0 MW
- Kano DisCo – 0 MW
- Port Harcourt DisCo – 0 MW
- Yola DisCo – 0 MW
Jimilla: 50 MW kacal aka rarraba a duk faɗin ƙasa, alhali bukatar wutar ta fi haka nesa ba kusa ba.
Tushen wutar lantarki ya sha lalacewa, inda a watan Oktoba, 2024 aka rahoto cewa tsuhen wutar lantarkin ya lalace sau 105 a tarihi, wanda a yanzu adadin ya haura haka.
Tushen wutar Najeriya ya lalace
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tushen wutar lantarki na kasa ya samu matsala, lamarin da ya haddasa katsewar wuta a wasu sassan Najeriya.
Tushen wutar lantarki wanda ya lalace a Maris din 2025, ya raunana murnar da gwamnatin Najeriya take yi na samar da wutar lantarki mai karfin 6,000MW.
A rahoton da aka fitar, an bayyana cewa samar da wutar lantarkin ya ragu daga 4,000MW zuwa kasa da 1,000MW da karfe 2:00 na ranar Juma'a, 7 ga Maris, 2025.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


