Jami'an Tsaro da Ƴan Bindiga Sun Gwabza Ƙazamin Faɗa a Malumfashi, An Rasa Rayuka
- Dakarun Operation Fansan Yanma tare da taimakon sauran jami'an tsaro sun fatattaki ‘yan bindiga a karamar hukumar Malumfashi
- A yayin da ake musayar wuta, 'yan ta'addan sun kashe shugaban mafarauta, Usman Lawal, sannan su ma an kashe masu mutum daya
- Harin na yammacin Talata, 9 ga Satumba, 2025, na zuwa ne bayan Gwamna Dikko Radda ya yi magana kan sulhu da 'yan bindiga a Katsina
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina – Rahotanni sun tabbatar da cewa dakarun Operation Fansan Yamma tare da sauran jami’an tsaro sun yi artabu da 'yan bindiga a Malumfashi.
An ce sojoji, 'yan sanda, 'yan sa-kai da jami'an C-Watch sun dakile harin da ‘yan bindigar suka kai kauyen Naalma, da ke a yammacin Talata.

Source: Twitter
Sojoji sun dakile harin 'yan bindiga a Malumfashi
Mai sharhi kan lamuran tsaro a Arewa maso Gabas da kuma yankin Tafkin Chadi, Zagazola Makama ne ya ruwaito labarin a shafinsa na X.
Rahoton ya yi nuni da ce jami’an tsaro sun amsa kiran gaggawa zuwa kauyen, inda suka yi musayar wuta ta dan dogon lokaci, kafin miyagun su tsere zuwa cikin daji.
Sai dai a yayin gumurzun, Usman Lawal, mai shekaru 35, wanda shi ne shugaban mafarautan yankin, ya samu mummunan raunin da ya yi sanadiyyar rasuwarsa.
An kuma kashe ɗan bindiga daya sannan aka kwato bindigar da aka kwace daga hannun shugaban mafarautan.
Rahotannin sun nuna cewa wasu daga cikin ‘yan bindigan sun gudu da harbin bindiga, lamarin da ya sa jami'an tsaro ke ci gaba da gudanar da sintiri da bincike a yankin.
An fafata tsakanin sojoji da 'yan bindiga
Wannan na zuwa ne kwanaki bayan 'yan bindiga sun yi yunkurin kai hari kauyen Tashar Gemu, da ke karamar hukumar Malumfashi.
Rahoton Daily Post ya nuna cewa dakarun Operation Fansan Yanma, 'yan sanda da jami'an C-Watch, sun tari 'yan bindigar, inda suka yi artabu.

Kara karanta wannan
'Duk da fara shirin sulhu, 'Yan bindiga sun yi kisa, an sace mutane masu yawa a Katsina
Wata majiya ta shaida cewa an yi dauki ba dadi a lokacin da 'yan bindigar suka shiga cikin kauyen, inda dakarun tsaron suka bude masu masu wuta, har suka tsere.
An rahoto cewa dakarun sun bi sawunsu har zuwa kauyen Unguwar Gambo, inda suka kashe ɗaya daga cikin ‘yan bindigan.

Source: Facebook
Kisan mutum 32 a Unguwar Mantau
Malumfashi dai tana fama da hare haren 'yan bindiga a 'yan kwanakin nan, inda a ranar 19 ga Agusta, 2025, 'yan bindiga suka kashe masallata 32 a garin Unguwar Mantau.
Wani mazaunin yankin ya shaida wa BBC Pidgin cewa mutum 25 aka kashe a masallaci bayan kammala sallar Asuba, yayin da wasu biyar suka samu raunuka.
Amma daga bisani, gwamnatin jihar Katsina, ta fitar da sanarwar cewa mutane 32 ne aka kashe a harin na Unguwar Mantau, mafi muni a Malumfashi a wannan shekara.
Gwamna ya magantu kan sulhu da 'yan bindiga
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Dikko Radda ya ce akwai batun tattauna wa da 'yan bindiga da ake yi don ganin an samu zaman lafiya a Katsina.
A cewar Gwamna Radda, an samu zaman lafiya a kananan hukumomi hudu da suka yi zaman sulhu da 'yan bindiga, inda wasu garuruwan ke shirin yin hakan.
Gwamnan jihar na Katsina ya fadi hakan ne yayin da ya kaddamar da wani shiri da zai farfado da yankunan da matsalar tsaro ta fi yi wa muni a Katsina.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

