Cocin Katolika Ya Fusata da Zanga Zangar Adawa da 'Ziyarar El Rufa'i' a Imo
- Cocin Katolika na Owerri ya karyata jita-jitar da aka yada a kan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i
- Jita-jitar ta fusata mutanen ijihar, inda su ka fusata, aka dauki takardu zuwa inda cocin ta gudanar da wani taron mai suna Odenigbo
- Labarin da aka rika yada wa ya ce El-Rufa'i ya gabatar da lacca a taron da dan kabilar Ibo ne kadai ke bude shi a kowace shekara
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Babban cocin Katolika da ke Owerri ya yi Allah-wadai da zanga-zangar da wasu suka tayar yayin taron laccar Odenigbo da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata.
Wasu fusatattun bayin Allah ne su ka fara zanga-zangar bayan an yi rade-radin cewa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yana cikin mahalarta taron.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa cikin wata sanarwa da Rabaran Fr. Patrick C. Mbarah, Sakatare/Kancler na Cocin ya fitar, ba El-Rufa'i ne ta gabatar da laccar Odenigbo a taron ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cocin Imo ta magantu kan Nasir El-Rufa'i
Rahoton ya ce a cewar cocin, ba a taba gayyatar Nasir El-Rufa'i don ya yi jawabi ko taron manema labarai ba.
Cocin ya ce an gabatar da laccar bana a cikin harshen Ibo kai tsaye, ta bakin Rev. Sr. Prof. Evangeline Oparaocha daga Jami’ar Fasaha ta Owerri.
Ya bayyana cewa yayin da ake tsakiyar lacca a Maria Assumpta Cathedral, wasu gungun matasa da mata, dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce, sun kutsa cikinsu.
Mutanen suna bayyana kalamai marasa dadi a kan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i da takwaransa na jihar Anambara Anambra, Peter Obi.

Source: Facebook
Ya ce:
“Wannan babban kuskure ne da rashin kunya. Wasu mutane da ba su san darajar wurin addini ba, sun dauki nauyin tada zaune tsaye da sunan zanga-zanga.”

Kara karanta wannan
'Talauci ya yi muni a Najeriya,' El Rufa'i ya ce akwai mafita kan matsin tattalin arziki
An yi kira ga gwamnatin Jihar Imo da hukumomin tsaro da su gano wadanda ke da hannu a wannan abu, tare da hukunta su domin hana irin hakan a nan gaba.
Cocin Imo ta kare Peter Obi
Hakanan, cocin ya kara da bayyana cewa Peter Obi, wanda ya saba halartar laccar, bai samu damar halarta bana ba.
Rabaran Mbarah ya ce laccar Odenigbo tana da tsarin da ake bi, wanda ya tanadi malamin addini daga kabilar Ibo ne kadai zai gabatar da ita kowacce shekara.
Ya kuma kara da cewa babu wani lokaci da aka shirya wa El-Rufai jawabi a Villa Assumpta ko kuma taron manema labarai.
Cocin ya bukaci 'yan jarida da sauran kafafen yada labarai da su guji yada jita-jita da labaran karya, tare da jaddada cewa Jihar Imo jiha ce mai zaman lafiya da karamci.
Ana shirin daukar mataki a kan El-Rufa'i
A baya, kun ji cewa rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta sake jaddada cewa dole tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El‑Rufai da wasu manyan jam'iyyar ADC su bayyana a gabanta.
An fara gayyatar El-Rufai da wasu jagororin jam’iyya tare da buƙatar su halarci CID don amsa tambayoyi a kan rikicin da ya faru a yayin wani taro da su ka gudanar a Kaduna.

Kara karanta wannan
Yaron El Rufa'i: Uba ya yi raddi ga kalamai da zarge zargen tsohon Gwamnan Kaduna
Rundunar ta jaddada cewa tsarin doka yana ba ta damar ɗaukar matakan tilastawa, har da kama wadanda aka gayyata idan suka ki zuwa CID domin amsa tambayoyin da su ka dace.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
