'Yan Bindiga Sun Shiga Uku, Gwamna Zai Gina Sabon Sansanin Sojoji na Musamman a Kebbi

'Yan Bindiga Sun Shiga Uku, Gwamna Zai Gina Sabon Sansanin Sojoji na Musamman a Kebbi

  • Gwamna Nasir Idris ya sanar da gagarumin shirin da ya yi na murkushe 'yan ta'adda da wanzar da zaman lafiya a jihar Kebbi
  • Mai girma gwamnan ya bayyana cewa zai kafa sansanin sojoji a karamar hukumar Augie domin karfafa tsaro da kare rayuka
  • Ya kuma ce za a yi cikakken gyara ga asibitin gwamnati na garin Augie domin inganta lafiyar al’umma daga matakin farko

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kebbi - Gwamnan Nasir Idris, ya bayyana shirin kafa sansanin sojoji na musamman a karamar hukumar Augie domin taimaka wa jami’an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya a Kebbi.

Ya sanar da hakan ne ranar Talata yayin wata walima ta musamman da aka shirya, lokacin kaddamar da sakatariyar jam’iyyar APC a Augie.

Gwamna Nasir Idris zai gina sabon sansanin sojoji a karamar hukumar Augie, jihar Kebbi
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris a bikin ranar tunawa da 'yan mazan jiya na shekarar 2024. Hoto: @NasiridrisKG
Source: Twitter

Gwamna zai gina sansanin sojoji a Kebbi

Kara karanta wannan

Tubabbun 'yan bindiga sun dawo shiga jama'a, kasuwa da asibiti a Kaduna

Gwamna Nasir Idris ya ce sabon sansanin sojojin zai taimaka wajen tabbatar da tsaro ga Augie ba, da makwabtan yankuna, inji rahoton AIT.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Mun kuduri aniyar tallafawa jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi a jihar Kebbi. Wannan sansanin soji zai taimaka wajen dawo da kwanciyar hankali ga jama'a."

- Gwamna Nasir Idris.

Garuruwan karamar hukumar Augie sun jima suna fuskantar hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane, wanda ake ganin sabon sansanin sojin zai iya kawo karshen hakan.

Baya ga batun tsaro, Gwamna Idris ya ce gwamnatin jihar za ta amince da cikakken gyaran asibitin gwamnati na Augie domin al’umma su samu ingantaccen kiwon lafiya a kusa da su.

Yaki da ta’addanci a Kebbi ta Kudu

A watan Yuni 2025, Gwamna Idris ya sanar da shirin kafa sansanin sojojin Najeriya a yankin Zuru domin magance hare-haren ‘yan bindiga da suka lakume rayuka a kauyukan Tadurga da Kyebu.

Gwamnatin jihar ta taimaka wajen kawo manyan motocin yaki da kayan aikin soja, tare da samar da wuri na wucin gadi ga dakarun soji kafin a gina sansaninsu, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan Kano ya gana da Sheikh Jingir kan rasuwar malamin Izala

Haka kuma, gwamnatin ta ce tana shirin gyara dokoki domin sanya hukunci mai tsauri, ciki har da hukuncin kisa ko daurin rai-da-rai ga wadanda aka kama suna taimakawa ‘yan bindiga.

Gwamna Nasir Idris ya sha daukar matakan da su samar da zaman lafiya ga garuruwan Kebbi
Taswirar jihar Kebbi da ke a Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An kaddamar da ofishin APC a Kebbi

A taron na ranar Talata, shugaban APC na jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Kana-Zuru, ya yaba da jagororin jam’iyyar a Augie bisa samar da sabuwar sakatariya, inda ya bukaci sauran kananan hukumomi su yi koyi da su.

A nasa jawabin, shugaban jam’iyya na karamar hukumar Augie, Alhaji Bashir Mera, ya ce an shirya walimar domin yin addu’ar neman tsarin Allah a mulkin Gwamna Idris.

Wani jigon jam’iyya a yankin, Barista Bello Abubakar Bayawa, ya bada gudunmawar mota Peugeot 406, babura guda 10 da injinan nika guda 10 domin tallafa wa jama’a.

'Babu sansanin 'yan bindiga a Kebbi' - Gwamna

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamnan Nasir Idris ya bayyana cewa babu wani sansanin 'yan bindiga da ya yi saura a jihar Kebbi.

Ƙauran Gwandu ya ce 'yan ta'adda na shigo wa Kebbi ne daga jihohin makota su farmaki jama'a su koma, amma ba su da sansani ko daya a jihar.

Kara karanta wannan

'Abubuwa 4 ne ke rura wutar ta'addanci,' Gwamna Uba Sani ya nemo mafita ga Arewa

Gwamnan ya ce zai samar da ƙarin kayan aiki ga ƴan banga domin inganta ayyukansu na taimakawa jami'an tsaron Najeriya wajen kakkabe miyagu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com