'Mazambaci ne': An Ji 'Gaskiyar' abin da Ya Sa Tinubu Ya Kori Hadiminsa, Umunubo

'Mazambaci ne': An Ji 'Gaskiyar' abin da Ya Sa Tinubu Ya Kori Hadiminsa, Umunubo

  • Shugaba Bola Tinubu ya tsige Fegho Umunubo daga mukamin mai taimaka masa kan tattalin arzikin zamani da kuma kirkire-kirkire
  • Wasu sababbin bayanai sun nuna cewa an kori Umunubo daga aiki bayan da aka same shi yana zambatar 'yan fim da masu kirkire-kirkire
  • Wata babbar zamba da aka ce ya aikata ita ce wacce ya kulla yarjejeniyar bogi da miliyoyin Naira da mai shirya fina finai, Arese Ugwu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Sababbin bayanai sun bayyana game da dalilin da ya sa Shugaba Bola Tinubu ya kori hadiminsa, Mista Fegho Umunubo daga aiki.

Fegho Umunubo ya kasance mai taimaka wa shugaban kasa kan tattalin arzikin zamani da kirkire-kire, karkashin ofishin mataimakin shugaban kasa.

Shugaba Bola Tinubu ya kori mai taimaka masa ta fuskar tatalin arzikin zamani da kirkire-kirkire.
Fegho Umunubo, tsohon mai taimaka wa shugaban kasa, da Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

Majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun shaida wa Premium Times cewa an tsige Umunubo bayan an gano yana da hannu a damfara iri-iri a masana’antar kirkire-kirkire, inda yake amfani da mukaminsa wajen yaudarar jama’a.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Bola Tinubu ya kori hadimin mataimakin shugaban kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zargin hadimin Tinubu da yaudarar 'yar fim

Daya daga cikin fitattun ddamfarar da ya yi ita ce yarjejeniyar tallafin kudi da ya kulla da marubuciya kuma mai shirya fina-finai, Arese Ugwu, wacce ta kirkiri shirin The Smart Money Woman.

Takardun da jaridar ta gani sun nuna cewa Umunubo ya rattaba hannu a kan yarjejeniyar bayar da N10m don tallata fim din Lara Unlimited, wanda Ugwu ta shirya.

Yarjejeniyar ta hada da tallata ofishin shugaban kasa a bangaren tattalin arzikin zamani ta hanyar saka sunan ofishin a jikin allon sanarwa, talla kafin a fara haska fim a sinima, da kuma shiga shirin podcast da ma tallata gwamnati.

Sai dai Umunubo bai taba cika wannan alkawari ba, kamar yadda a ranar 30 ga watan Agusta, 2025, Arese Ugwu ta fito fili ta zarge shi da damfara a shafinta na Instagram.

Kara karanta wannan

Romon siyasa: Kansila ya naɗa sababbin hadimai 18, ya raba masu wurin aiki a Kaduna

Mai shirya fina finan ta rubuta cewa:

“Ni karan kaina ina bin sa bashin N10m. Amma ba a kan wannan nage magana ba, ina magana kan yaudarar mutane da ya rika yi kan tallafin $617m da N5bn da ya dade yana jingina wa ofishin mataimakin shugaban kasa alhali ba shi da ikon yin hakan.”

Amfani da mukami wajen yaudarar mutane

Majiyoyi sun ce ya saba yin irin wannan yaudarar, inda ya sha daukar wa ‘yan Nollywood alkawura da ya gaza cika wa, yana amfani da kusancinsa da gwamnati wajen samun amincewar su, yana ba su kwangila ba tare da ya biya ba.

Wani daga cikin majiyoyin ya ce:

“Ya damfari mutane da dama a masana’antar ta hanyar amfani da ofishin nan nasa.”

An ce korafe korafen da 'yan Nollywood da sauran 'yan masana'antar kirkire-kirkire kan Umunubo ta yi yawa, wanda ya je kunnen shugaban kasa.

'Yan fim sun zargi tsohon hadimin Tinubu, Fegho Umunubo da zambatarsu.
Mai shirya fina-finai, Arese Ugwu, tare da tsohon hadimin shugaban kasa, Umunobo a wajen kaddamar da wani fim a Legas. Hoto: @smartmoneyarese
Source: Instagram

Martanin hadimin bayan Tinubu ya kore shi

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamnan Kano ya gana da Sheikh Jingir kan rasuwar malamin Izala

Wasu majiyoyin sun ce tun a watan Agusta, 2025, aka kori Umunubo, amma ya ci gaba da bayyana kansa a matsayin mai taimaka wa shugaban kasa, abin da ya tilasta wa fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwa a hukumance ranar Litinin.

An tuntubi tsohon hadimin shugaban kasar, Umunubo ta hanyar Instagram kan wadannan zarge zarge amma bai amsa ba.

Sai dai, bayan fitarwar gwamnati na dakatar da shi, ya wallafa cewa:

“Girmamawa ce sosai a gare ni na yi wa wannan kasa mai girma da masana’antar kirkire-kirkire hidima.”

Tinubu ya yanke alaka da hadiminsa

Tun da fari, mun ruwaito cewa, a ranar Litinin, fadar shugaban kasa ta sanar da korar Fegho Umunubo daga aiki, matsayin hadimin shugaban kasa.

Daraktan yada labaran gwamnati, Abiodun Oladunjoye, ya fitar da sanarwar tsige Umunobi daga mukamin mai taimaka wa shugaban kasa kan tattalin arzikin zamani da kirkire-kire.

Gwamnatin tarayya ta yi gargadi ga masu ruwa da tsaki a harkokin kirkire-kirkire da kada su guji yin hulda da shi, don ba shi da wata alaka da gwamnati yanzu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com