Rashin Tsaro: Sarkin Gargajiya Ya Bukaci a Yi Azumin Mako 2

Rashin Tsaro: Sarkin Gargajiya Ya Bukaci a Yi Azumin Mako 2

  • Oba na Benin, Ewuare II, ya umarci ‘yan asalin Edo da mazauna jihar su shiga azumi da addu’a daga 15 zuwa 28 ga Satumba, 2025
  • Manufar azumin ita ce neman kariya daga sharri, samun zaman lafiya, da samun amfanin gona mai yawa a daminar bana
  • Umarnin ya zo ne a lokacin da jihar ke fama da matsalolin tsaro ciki har da kisan jami’an NSCDC a Okpella a makon da ya wuce

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Edo - Oba na Benin, Mai Martaba Ewuare II, ya bayyana wani mataki domin jihar Edo ta samu kariya daga matsaloli da kuma cigaba.

Ya bukaci dukkan ‘yan asalin jihar da mazauna ciki da wajen Edo, da su fara azumi da addu’a na tsawon mako biyu.

Kara karanta wannan

'Talauci ya yi muni a Najeriya,' El Rufa'i ya ce akwai mafita kan matsin tattalin arziki

Oba Ewuare II yayin da ya kai ziyaya fadar shugaban kasa
Oba Ewuare II yayin da ya kai ziyaya fadar shugaban kasa. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da jihar ke fuskantar matsalolin tsaro, ciki har da kisan jami’an tsaro a Okpella.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarki ya bukaci a yi azumi a Edo

Sanarwar da Obamedo na Benin, Efosa Igbinomwanhia, ya fitar ta ce azumin zai gudana daga 15 zuwa 28 ga Satumba, 2025 daga karfe 6:00 na safe zuwa 6:00 na yamma kowace rana.

Oba Ewuare II ya ce wannan al’ada ce ta dade tana gudana kafin bikin girbe doya da ake yi a jihar Edo.

Ana azumin ne domin rokon Allah ya sa albarka a girbin da za a yi a karshen damina da kuma tsare rayukan al’umma daga mutuwa kwatsam.

Ya kuma roki al’ummar Benin da ke cikin gida da waje su shiga wannan ibada, domin samun kwanciyar hankali da farin ciki a jihar da kasa baki daya.

Manufar addu’a da azumi a Edo

Kara karanta wannan

2027: ADC ta fadi tsoron da APC ta ji bayan kai wa 'yan adawa hari a wajen ibada

Sarkin ya bayyana cewa wannan azumi zai taimaka wajen kawo zaman lafiya, kwanciyar hankali da nasara ga al’ummar jihar.

Ya ce manufar ita ce hada kan kowa domin rokon Allah ya kare jihar daga cututtuka, rikice-rikice, da matsalolin tsaro da suka addabi al’umma.

Ya kuma jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin al’umma a gida da wajen kasa wajen yin wannan ibada.

Ana fama da matsalar tsaro a Edo

Sanarwar ta zo ne bayan wani hari da ya girgiza jihar makon da ya gabata, inda ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka kashe jami’ai takwas na NSCDC a Okpella.

Vanguard ta wallafa cewa harin ya kuma jawo mutuwar jami’an tsaro yayin da aka yi garkuwa da wani mutum dan kasar China daga kamfanin simintin BUA.

Gwamnan Edo yana magana a wani taro
Gwamnan Edo yana magana a wani taro. Hoto: Edo State Goverment
Source: Facebook

Gwamna ya yi hudubar Juma'a a Nasarawa

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya jagoranci sallar Juma'a a wani masallaci.

Abdullahi Sule ya jagoranci hudubar ne yayin da aka kaddamar da masallacin da wani kwamishinansa Kirista ya gina.

Manyan 'yan siyasa ciki har da tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu sun halarci bude masallacin da aka yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng