Sababbin Hotuna Sun Nuna irin Sauye Sauyen da Aka Yi wa Kabarin Buhari a Daura
- Gwamna Dikko Radda da wasu mukarraban gwamnatin Katsina sun ziyarci kabarin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura
- Bashir Ahmad, ya tabbatar da wannan ziyarar tare da wallafa sababbin hotunan da suka nuna sauye sauyen da aka yi wa kabarin Buhari
- 'Yan Najeriya sun yi martani kan irin sauyin da aka gani a kabarin, da yadda shugabanni ke ci gaba da kai wa kabarin Buhari ziyara
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina - Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya kai ziyara ta musamman zuwa kabarin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a gidansa da ke Daura.
A yayin ziyarar da Gwamna Radda tare da tawagar manyan jami'an gwamnatinsa suka kai ranar Litinin, sun yi addu'a don neman rahama ga mamacin.

Source: Twitter
Mai ba Buhari shawara na musamman kan kafofin sadarwa na zamani, Bashir Ahmad, ya bayyana hakan a shafinsa na X, inda ya wallafa hotunan sauye-sauyen da aka yi wa kabarin Buhari.

Kara karanta wannan
Bayan tsawon lokaci, gwamna ya tabbatar da fara tattaunawar sulhu da 'yan bindiga
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Radda ya ziyarci kabarin Buhari
Gwamna Radda ya roki Allah (SWT) da ya gafarta wa Buhari, ya karɓi kyawawan ayyukansa, ya kuma sanya shi a Aljannatul Firdaus.
Gwamnan ya kuma yi addu'a ga al'ummar Musulmi, tare da rokon Allah ya saukar da zaman lafiya da hadin kai ga jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya.
Sanarwar Bashir Ahmad ta ce:
"Gwamnan Katsina, Dr. Dikko Umar Radda, a yau, bisa rakiyar wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatinsa, sun ziyarci kabarin jagoranmu, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
"Sun yi addu'o'i ga marigayin, tare da nema masa gafarar Allah, da kuma roka masa yafiyar Allah a kan kura-kuransa."
Dalilin Radda na zuwa kabarin Buhari
Ziyarar Gwamna Radda ta zo ne a wani ɓangare na tafiyarsa zuwa Masarautar Daura don halartar bikin Hawan Magajiya na Sallar Gani da ake yi shekara-shekara, inji rahoton Premium Times.
Sallar Gani wani muhimmin biki ne na al'ada da addini wanda Majalisar Masarautar ke shiryawa don tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).
Wannan mataki na Gwamnan na nuna girmamawarsa ga tsohon shugaban kasa, Buhari da kuma jajircewar gwamnatinsa wajen haɓaka addini, haɗin kai, da al'adu a faɗin Katsina.

Source: Twitter
An ga sauye sauye a kabarin Buhari
Bayan da Bashir Ahmad ya wallafa hotunan wannan ziyara, 'yan Najeriya sun yi martani kan sauye sauyen da suka gani a kabarin Buhari:
@Abou_Humairah:
"Haka suka mayar da kabarin Buhari?"
@muhammad3933:
"Buhari ya zama shehi ne ake zuwa neman tabarrakinsa?😂"
@Aliyutsiga:
"Duk wannan kwalliyar fa ba za ta amfani mamaci da komai ba."
@JemeelS:
"Yadda ake ci gaba da kawata kabarin Buhari, sai dai mu roki Allah ya gyara imaninmu, ya kuma kara mana fahimtar Sunnah."
@AboladeOlaniran:
"Sun yi daidai da suka katange wajen."
@amigo12233:
"Sun fi kula da kabarinsa a kan rayukan rayayyu. Hmm."
@Bserious8:
"Duk wannan abin da ake yi gwara ayi ta nema masa yafiya a gurin 'yan Nigeria, ya fi alheri sama da gyara masa kabarinsa"
Kalli hotunan a kasa:
Atiku, El-Rufai sun ziyarci kabarin Buhari
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da Malam Nasir El-Rufai sun ziyarci kabarin Muhammadu Buhari.
'Dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, shi ma an ce ya ziyarci garin Daura domin miƙa ta’aziyya ga iyalan tsohon shugaban ƙasar.
Manyan Najeriya na ci gaba da kai ziyara kabarin Muhammadu Buhari domin yi masa addu'a da kuma neman masa rahamar Allah a sabon makwancinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

