Mamakon Ruwan Sama da Zai Sauka Ranar Talata Zai Jawo Ambaliya a Jihohin Arewa 2

Mamakon Ruwan Sama da Zai Sauka Ranar Talata Zai Jawo Ambaliya a Jihohin Arewa 2

  • Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama tare da iska mai karfi a jihohin Arewa, a ranar Talata, 9 ga Satumba, 2025
  • NiMet ta ce ruwan sama kamar da bakin kwarya da zai sauka zai iya jawo ambaliya a wasu jihohin Arewa ta Tsakiya kamar Neja da Kogi
  • A Kudu, jihohin Lagos, Ogun, Edo, Cross River da Akwa Ibom za su fuskanci ruwan sama mai yawa, wanda zai iya haddasa ambaliya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Hukumar da ke kula da hasashen yanayi ta kasa (NiMet) ta fitar da hasashen yanayi na ranar Talata, 9 ga watan Satumba, 2025.

Hasashen hukumar ya nuna cewa za a samu ruwan sama mai yawa, wanda zai sauka hade da iska mai karfi da tsawa, kuma zai jawo ambaliya a sassan kasar.

Kara karanta wannan

'Talauci ya yi muni a Najeriya,' El Rufa'i ya ce akwai mafita kan matsin tattalin arziki

Hukumar NiMet ta ce ruwan sama mai karfi da zai sauka zai jawo ambaliya a jihohin Arewa
Jami'ain agaji na kokarin ceto wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su. Hoto: Sani Hamza / Staff
Source: Original

Hukumar NiMet ta wallafa rahoton hasashen a shafinta na X a daren ranar Litinin, tana mai yin gargadi ga mazauna garuruwan da ke bakin koguna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hasashen ruwan sama a yankin Arewa

NiMet ta bayyana cewa za a samu ruwan sama a safiyar Talata, a jihohin Taraba, Adamawa, Kebbi, Zamfara, Gombe, Bauchi, Kaduna, Sokoto da Katsina.

Hukumar ta ce a jihohin Borno, Sokoto, Kebbi, Bauchi, Kaduna, Adamawa, Jigawa, Kano, Katsina, Zamfara da Taraba za su sake samun ruwan sama mai yawa a yammacin Talata.

Wannan mamakon ruwan sama da za a yini ana yi, zai iya jawo tsaiko ga matafiya, yayin da iska da ruwa mai karfi ka iya jawo hadurran ababen hawa.

Hasashen ruwan a sauran jihohin Arewa

A yankin Arewa ta Tsakiya kuwa, hasashen ya nuna cewa za a samu ruwan sama mai sauƙi a wasu sassan Abuja, Kwara, Benue, Neja da Kogi tun daga safe.

Kara karanta wannan

NiMet: Bayan kusufin wata, za a yi guguwa da ruwa a Kano, wasu jihohin Arewa

A yammacin ranar kuwa, ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi zai sauka a Nasarawa, Neja, Filato, Kogi, Kwara, Benue da Abuja.

NiMet ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar a samu ambaliyar ruwa musamman a Neja da Kogi, inda ruwa ya cika tafkuna da manyan kogunan yankin.

Hasashen yanayi a Kudancin Najeriya

A kudancin Najeriya, NiMet ta ce za a fara da yayyafi a Ebonyi, Imo, Abia, Oyo, Ogun, Edo, Legas, Cross River da Akwa Ibom a safiyar Talata.

Daga baya kuma, ruwan sama mai karfi zai sauka a yawancin ranar a kusan dukkanin jihohin Kudancin kasar.

Hukumar NiMet ta ce iska mai karfi yayin da ake ruwan sama za ta iya jawo hadurran ababen hawa.
Abubuwan hawa na tafiya kan titi yayin da ake ruwan sama, da sararin samaniya yayin da ake walkiya. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Shawarar hukumar NiMet ga 'yan Najeriya

NiMet ta shawarci jama’a da su kasance cikin shiri, musamman masu zirga-zirga a manyan tituna saboda iska mai ƙarfi na iya rage gani da janyo hadurra.

Hakanan, hukumar ta bukaci al’ummar da ke rayuwa a wuraren da ke da koguna musamman a Neja da Kogi da su dauki matakan kariya daga hadarin ambaliya.

An samu mummunar ambaliya a Taraba

A wani labarin, mun ruwaito cewa, akalla garuruwa bakwai ne suka nutse a cikin ruwa, bayan afkuwar wata mummunar ambaliya a jihar Taraba.

Kara karanta wannan

Najeriya, ƙasashe 9 za su fuskanci kusufin wata, an ji tsawon lokacin da zai dauka

Kauyukan da ambaliyar ta shafa sun hada da garin Kunini a karamar hukumar Lau, inda ta rusa gidaje, ta lalata gonaki kuma ta hallaka dabbobi.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA ta sanar da cewa SEMA a Taraba ta kwashe wasu mazauna Lau da Jalingo zuwa wuri mai aminci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com