‘Zai Iya Komawa ga Opay’: Ran Melaye Ya Baci kan Yawan Cin Bashi da Tinubu Ke Yi
- Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya soki yawan bashi da gwamnatin Bola Tinubu ke karba, yana cewa hakan matsala ne
- Melaye ya zargi shugaban kasar da sayen jirgin ruwa, jirgin sama da motocin alfarma a lokacin yunwa, yana kiran a kawo sauyi
- Yake cewa Majalisar Tarayya ta samu karin kasafi zuwa N300bn, yana mai gargadin cewa kudin da ake karbo bashi bai da ma’ana
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lokoja, Kogi - Tsohon Sanatan Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya bayyana damuwa kan yawan cin bashi da ake yi a Najeriya a halin da take ciki.
Melaye ya bayyana matsaloli game da yawan bashin da Shugaba Bola Tinubu ke karbowatun bayan hawansa kan mulki a Mayun 2023.

Source: Facebook
Dino Melaye ya gargadi Tinubu kan cin bashi
A hirar da ya yi a shirin Prime Time na Arise TV ranar Litinin, Melaye ya kalubalanci dalilin cin bashin dala biliyan 1.7 daga Bankin Duniya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Melaye ya yi gargadi cewa idan ba a kula ba, Tinubu na iya fara neman bashi daga manyan kamfanonin kudi na kasar, kamar Opay da Moniepoint.
Ya mayar da martani ne kan damuwar da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas ya nuna na rashin jin dadin yawan bashi daga gwamnatin Tinubu.
Sai Rt. Hon. Abbas daga bisani ya yi magana inda ya ce an yi masa mummunanr fahimta ba haka yake nufi ba saboda babu kasar da ba ta cin bashi, Vanguard ta ruwaito.
Dino Melaye ya ce majalisar tarayya ta riga ta amince da cin bashin fiye da dala biliyan 21, tare da wasu karin bukatu.
Melaye ya bayyana:
“Wannan gwamnati ce mafi sakaci a tarihi, shugaban da ya ce zai rage barnar kudi, ya siya jirgin ruwa.
“Jirgin ruwan da shugaban ya siya bai taba shiga yankin Najeriya ba, yana tsakanin Monaco da Paris kawai.”
Ya kuma tambayi dalilin sayen jirgin ruwa da jirgin sama a lokacin da talauci da yunwa ke addabar jama’a a fadin kasa, Daily Post ta ruwaito.
Melaye ya jaddada cewa daga zamanin Tafawa Balewa, Nnamdi Azikiwe har zuwa Muhammadu Buhari, an yi amfani da mota kirar Mercedes S-Class a matsayin motar shugaban kasa.
Ya kara da cewa:
“Yanzu shugaba Tinubu yana amfani da motar da Trump ke amfani da ita a Amurka, amma yana ikirarin rage facaka.
“Shugaban da ya ce zai kawo sauyi ya siya jirgi, ya siya motar alfarma, ya karawa Majalisa kudi, ya kuma ciwo bashi.
“Idan kuna samun karin kudi, me yasa kuke cin bashi? Har ma kakakin majalisa na APC yana nuna damuwa kan bashin.”
Ana zargin Melaye da rashin biyan haraji
Mun ba ku labarin cewa ana zargin cewa tsohon sanatan Kogi, Dino Melaye ya shafe shekaru biyu yana guje wa biyan harajin kudin da ya samu.
Hukumar haraji ta Abuja (FCT-IRS) ta ce Dino Melaye ya ki biyan harajin fiye da Naira miliyan 509 na kudaden shigarsa.
An gurfanar da Dino Melaye gaban kotu, kuma zai iya fuskantar hukuncin biyan harajin da wasu tara da za a ci shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

