'Yan Ta'adda Sun Yi Dirar Mikiya a kan Mazauna Zamfara, Sun Kashe Mutane

'Yan Ta'adda Sun Yi Dirar Mikiya a kan Mazauna Zamfara, Sun Kashe Mutane

  • ‘Yan bindiga sunkai harin ba zata wani yanki na karamar hukumar Gusau da ke jihar Zamfara inda su ka bude wa jama'a wuta
  • Rahotanni sun bayyana cewa jama'a na tsaka da tafiyar da harkokinsu a yammacin Lahadi, sai kawai su ka ji harbi ta ko ina
  • Mutane sun dimauce, inda su ka rika gudun neman mafaka, amma duk da haka an salwantar da rayukan bayin Allah haka kurum

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara – Rahotanni daga jihar Zamfara sun bayyana cewa wasu ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a kauyen Unguwar Kade.

Harin da aka kai Mada, a karamar hukumar Gusau, da daren Lahadi ya fitar da jama'a daga cikin hayyacinsu saboda fargaba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna a Katsina, an samu asarar rayuka

An kashe jama'a a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa maharan sun kashe mutane uku a lokacin da aka kai harin nan take.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan ta'adda sun kai hari a Zamfara

Wani mazaunin yankin da ya nemi a boye sunansa ya shaida wa manema labarai cewa harin ya faru ne da misalin karfe 3:00 na rana.

Rahotanni sun nuna cewa mazauna kauyen na cikin harkokinsu na yau da kullum, sai kawai ‘yan bindigar suka mamaye su, su ka bude wuta ba tare da bata lokaci ba.

Yan ta'adda sun tsere kafin zuwan sojoji
Hoton wasu daga cikin sojojin Najeriya Hoto: HQ NigeriaN Army
Source: Facebook

A yayin da jama'a ke gudun neman tsira ne kuma aka kashe mutum uku har lahira tare da jikkata wasu guda uku a gefe guda.

Bayan samun rahoton harin, hadakar jami’an tsaro da mafarauta daga yankin an tura su cikin gaggawa zuwa Unguwar Kade.

Sojoji da 'yan ta'adda sun yi sabani

Rahoton ya kara da cewa kafin jami'an tsaro da na sa kai su isa kauyen, 'yan bindigar sun yi layar zana bayan sun kammala barna a yankin.

Kara karanta wannan

Halin da ake ciki a Sokoto da fusatattun matasa suka farmaki mataimakin gwamna

Jami’an tsaro sun tabbatar da cewa gawarwakin wadanda suka mutu da kuma wadanda suka jikkata an garzaya da su asibiti domin a yi musu binciken likita da ba su kulawa ta gaggawa.

Wani jami’in tsaro da ke da masaniya kan lamarin ya ce an kara kaimi a sintirin hadin gwiwa a yankin domin dakile yiwuwar kawo wani harin.

Ya kara da cewa ana ci gaba da zurfafa bincike domin gano wadanda suka aikata wannan ta’asa tare da kama su.

Jihar Zamfara na daga cikin jihohin da ke fama da matsalar ‘yan bindiga, musamman a yankunan karkara, inda ake kai hare-hare kan al’ummomi da sace mutane don neman kudin fansa.

Sojoji sun hallaka dan ta'adda

A baya, mun wallafa cewa wasu 'yan bindiga sun gwabza fada da juna a cikin daji, lamarin da ya jawo asarar rayukan mayaka da dama a Zamfara.

A cewar majiya daga rundunar tsaro, lamarin ya faru ne a gabashin kauyen Magana Mai Rake, kusa da Yar Tashar Sahabi, a yankin Dansadau da ke Maru.

Fitaccen 'dan bindiga, Kachalla Abu Dan Barka, ya rasa ransa tare da mayaƙansa huɗu a harin kwanton bauna da aka musu yayin da suke rangadi a cikin daji.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng