‘Mu 2 ne Kadai a Duniya’: Malami Ya ce Idan Ya Mutu Gawarsa Firewa Za Ta Yi
- Shahararren Fasto a Najeriya ya tayar da kura a kafofin sadarwa bayan sanar da yadda zai mutu idan lokacinsa ya yi
- Fasto Chukwuemeka Ohanaemere, wanda aka fi sani da Odumeje, ya ce bayan mutuwarsa ba za a ga gawarsa ba, za ta tashi sama
- Ya bayyana kansa a matsayin zaki, yana mai cewa aikinsa bai shafi tsawon rai ba, sai cika manufar Ubangiji kawai a rayuwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Onitsha, Anambra - Kamar yadda ya saba, fitaccen Fasto a Najeriya ya bayyana abin da zai faru da gawarsa bayan ya mutu.
Jagoran cocin Mountain of Holy Ghost Intervention, Onitsha, Fasto Chukwuemeka Ohanaemere shi ya yi wannan jawabi yayin huduba a coci.

Source: Instagram
Fasto ya rikita mutane game da mutuwarsa
Faston wanda aka fi sani da Odumeje, ya jawo ce-ce-ku-ce bayan ya bayyana abin mamaki kan rayuwarsa da aikinsa, kamar yadda Tribune ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani wa’azi, ya ce lokacinsa a duniya ya ƙare, kuma “babu wanda zai ga gawarsa,” yana mai cewa manufarsa cika umarnin Ubangiji ne.
Ya ce:
"Ni ne mutum na biyu mafi girma a bangaren ruhi, dayan shi ne zaki wanda ya riga ya mutu, ba ni da wani lokaci sosai da zan sake batawa.
Ni ne mafi ƙarfi a cikin ruhaniya a duniya bayan Janar, Emmanuel TB Joshua, ba mu da yawa, mu biyu ne kawai, daya ya kammala aikinsa ya koma."

Source: Instagram
Fasto Odumeje ya fadi dalilin kafa cocinsa
Limamin ya ce an kafa cocinsa domin “cirewa mutane shakku kan Yesu,” inda ya bayyana saƙonsa a kan ikon Ubangiji da wahayi guda ɗaya.
Ya tabbatar da cewa bautawa Ubangiji shi kadai ake yi kuma wannan abin bauta din ba kowa ba ne sai Yesu Almasihu, Daily Post ta tabbatar a rahotonta.
A cewarsa:
“Babban abin da muka sanya a gaba shi ne wayar da kan mutane da cire musu shakku kan Yesu.
"Sannan mu tabbatar da cewa an bautawa Ubangiji shi kadai da ikonsa kuma wannan mutumin shi ne Yesu."
Yadda salon wa'azinsa ke tayar da kura
Odumeje ya shahara da salo na ban mamaki da furuci masu sosa rai, yana bayyana kansa da lakabi na sunaye daban-daban.
Faston ya yi kaurin suna wurin tayar da kura musamman a kafofin sadarwaa saboda yadda salon wa'azinsa yake a Najeriya.
Hakan ne ma ya sa yake da yawan mabiya a shafukan sadarwa wanda mabiyansa ke nuna jin dadi game da salon wa'azinsa.
Fasto zai fito takara da Tinubu a 2027
A baya, mun ba ku labarin cewa malamin coci, Fasto Chukwuemeka Ohanaemere ya bayyana kudurinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.
A yayin wata huduba mai zafi da ya gabatar ga mabiyansa, Fasto Odumeje ya bayyana cewa Najeriya na bukatar shugaba mai jini a jika.
Bidiyon da ke nuna lokacin da Fasto Odumeje ya nuna sha'awar tsayawa takara ya yadu sosai, ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a.
Asali: Legit.ng

