Tinubu Ya Waiwayi Daliban da Aka Sace Lokacin Jonathan, Ya ba Su Tallafin N1.85bn
- Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ware Naira biliyan 1.8 domin ilimantar da 'yan matan Chibok da kuma gyara halayensu
- An ce za a yi amfani da kudin don biyan kudin makaranta, masauki, sana'o'i, da tallafin gyaran halayensu su har zuwa 2027
- Gwamnatin tarayya ta bayyana dalilin da ya sa ta waiwayi daliban Chibok din da aka fara sace su a mulkin Goodluck Jonathan
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sanar da ware N1,854,277,768 domin samar da ilimi da kuma gyara halayen 'yan matan makarantar Chibok da kungiyar Boko Haram ta sace a 2014.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ilimi ta fitar, ta ce kudaden wani bangare ne na shirin tallafawa ‘yan matan Chibok da Boko Haram ta sace.

Source: Twitter
Za a kashe N1.85 kan 'yan matan Chibok
Jaridar Punch ta ce za a yi amfani da kudin wajen biyan kudin makaranta, masauki, horon sana'o'i, gyaran halayen su, da wasu ayyuka, wanda za a gudanar har zuwa 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daraktan yada labarai da hulda da jama'a na ma'aikatar ilimi ta tarayya, Boriowo Folasade, ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis.
A cewar sanarwar, ministan ilimi, Dr Tunji Alausa, ya ce za a biya tallafin ne a karkashin shirin "Renewed Hope" na shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Dr. Tunji Alausa ya ce wannan tallafi ya nuna jajircewar gwamnatin Tinubu wajen kare ilimi da makomar yaran da suka fuskanci sauyin rayuwa 'yan Najeriya.
Sanarwar ta ce:
"A karkashin shirin "Renewed Hope" na Shugaba Bola Tinubu, gwamnatin tarayya na tabbatar da cewa 'yan matan da aka ceto guda 108 za su ci gaba da samun cikakken gyaran hali da tallafin karatu."
An kai 'yan matan Chibok jami'ar Atiku
Ma’aikatar ta ce 68 daga cikin 'yan matan Chibok da aka ceto a halin yanzu an shigar da su Jami’ar Amurka ta Najeriya da ke Yola, wadda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya mallaka.
Ma'aikatar ta ce za a ci gaba da biyan kuɗin makaranta da masaukinsu a AUN, inda ta jaddada cewa fifikon gwamnati shi ne tabbatar da cewa ilimin ‘yan matan bai tsaya ba.
Sanarwar ta bukaci 'yan Najeriya da 'yan siyasa da su goyi bayan kokarin gyara halayyar 'yan matan da suka sha wahala hannun Boko Haram, inji rahoton Channels TV.

Source: UGC
Manufar tallafin Tinubu ga daliban Chibok
Ana fargabar cewa daga cikin 'yan mata 276 da aka sace, har yanzu 87 na hannun 'yan ta'addar, ba tare da sanin ko sun mutu ko suna raye ba.
A lokacin da lamarin ya faru, an sace 'yan matan ne a ranar 14 ga Afrilu, 2014, lokacin mulkin Goodluck Jonathan, a makarantarsu da ke Chibok, jihar Borno.
Wannan lamari dai ya ja hankalin duniya, kuma ya haifar da kokari na tsawon lokaci daga gwamnatoci, da kungiyoyin farar hula, da iyalai don ganin an ceto daliban, gyaran tarbiya.
Wannan tallafin kudin na yanzu, zai taimaka wajen dorewar ayyukan gyaran hali da kuma tabbatar da samun ilimi ga 'yan matan da aka ceto.
'Yan matan Chibok sun dawo da 'yaya 34
A wani labarin, mun ruwaito cewa, yayin da aka cika shekara 10 da sace ƴan matan Chibok, har yanzu wasu na tsare a hannun ƴan ta'addan Boko Haram.
Wasu daga cikin ɗaliban da aka sako sun dawo gida da yara 34, kamar yadda gidauniyar Murtala Muhammed (MMF) ta bayyana wa manema labarai.
Gidauniyar ta koka matuƙa dangane da auren dole da aka yi wa ƴan matan, yayin da suka gabatar da buƙatarsu a gaban gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng


