Jerin Jihohin da Mafi Karancin Albashi Ya kusa N100,000 ko sama da haka a Najeriya
A watan Yuli, 2024, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan dokar sabon mafi karancin albashi na kasa.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Hakan ya biyo bayan amincewar da Majalisar Tarayya ta yi da sabon kudirin albashin, wanda ya kunshi biyan ma'aikata albashi mafi karanci N70,000.

Source: Facebook
Dokar sabon mafi karancin albashi a Najeriya
Channels tv ta tattaro cewa sabuwar dokar albashin da Bola Tinubu ya sa hannu a wannan rana, ta kara mafi karancin albashi daga N30,000 zuwa N70,000.
Bayan haka ne, gwamnonin jihohi suka fara aiwatar da wannan doka, inda wasu suka amince da abin da ya haura N70,000.
A wannan shekara ta 2025 da muke ciki, an samu gwamnoni biyu da suka sake kara mafi karancin albashi daga N70,000.
Ana ganin wadannan gwamnoni sun yi haka ne domin inganta walwalar ma'aikata duba da halin matsin tattalin arziki da kuncin rayuwa da ake ciki.
Jerin jihohi 4 da aka fi biyan albashi mai tsoka
A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro maku jihohin da ake biyan karamin ma'aikaci kusan N100,000 ko abin da ya haura haka. Ga su kamar haka.
1. Jihar Imo
Jihar Imo ce a sahun gaba a wannan rahoto bayan Gwamna Hope Uzodinma ya amince da N104,000 a matsayin mafi karancin albashin ma'aikata.
Gwamnan ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne domin gina alaka mai kyau da 'yan kwadago, da kuma inganta jin dadin al’ummar jihar baki ɗaya.

Source: Twitter
TVC News ta ruwaito cewa Uzodinma ya yi wannan kari ne bayan tattaunawa da kungiyoyin kwadago a gidan gwamnatinsa da ke Oweeri.
Uzodinma, wanda shi ne shugaban gwamnonin APC, ya kara da cewa daga 2020 zuwa yanzu, kudin da Imo ke samu daga tarayya sun ninka, daga N5bn–7bn zuwa N14bn.
2. Jihar Ebonyi
Gwamna Francis Nwifuru ya bi sahun takwaransa na jihar Imo, ya kara mafi karancin albashin ma'aikatan gwamnatin Ebonyi daga N70,000 zuwa N90,000.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na jihar, Cif Ikeuwa Omebe, ne ya bayyana hakan a gidan gwamnati bayan taron Majalisar Zartarwa ta jiha.

Source: Facebook
A cewar Omebe, sabon mafi karancin albashi na N90,000 zai fara aiki nan take kuma ya shafi dukkan rukunan ma’aikatan gwamnatin Ebonyi, kamar yadda Tribune ta rahoto.
3. Jihar Legas
Gwamna Babajide Sanwo-Olu, ya amince da biyan ma'aikatan jihar Legas N85,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi.
Ya sanar da haka ne ranar Laraba, 16 ga watan Oktoba, 2024, inda ya ce bayan wasu ƴan watanni zai kuma ƙara albashin zuwa N100,000.
Mai girma gwamnan ya ce ma'aikata sun cancanci a rika biyansu adadin kudin da za su ɗauke ɗawainiyar su da ta iyalansu a wata inji rahoton Bussiness Day.

Source: UGC
Legit Hausa ta kawo rahoton cewa gwamnan Legas ya yi alkawarin fara biyan N100,000 a matsayin mafi karancin albaahi daga watan Janairu, 2025, amma dai har yanzu babu wata sanarwa da ta nuna ya cika.
4. Jihar Ribas
A jihar Ribas kuwa, Gwamna Siminalayi Fubara wanda aka dakatar a yanzu, ya fara biyan ma'aikata albashin akalla N85,000.
Gwamnatin Ribas ta ce Fubara ya amince da sabon albashin ne bayan ganawar sirri da kungiyoyin kwadago a gidan gwamnatinsa da ke Fatakwal.

Source: Facebook
A rahoton da Leadership ta kawo, shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar Ribas, George Nwaeke, ya ce zai taimaka matuka wajen rage wahalhalu da matsin da ma’aikata ke fuskanta.
'Yan kwadago sun fara neman karin albashi
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar kwadago (NLC) ta fara kiraye-kirayen a kara mafi karancin albaahi saboda taadar rayuwar da ake fama da ita a kasar nan.
Shugabar NLC ta jihar Legas, Hajiya Funmi Sesi ta bukaci Gwamna Sanwo-Olu ya iara albashin daga N85,000 zuwa N150,000 domin inganta walwalar ma'aikata.
Ta bayyana cewa kudin haya, sufuri, abinci da sauran buƙatun yau da kullum sun fi tsada a Legas fiye da sauran jihohin ƙasar nan, don haka akwai bukatar gwamnati ta duba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


