'Yan Sandan Jihohi: Gwamnonin Arewa Sun Hade, Sun Mara wa Kudirin Tinubu baya

'Yan Sandan Jihohi: Gwamnonin Arewa Sun Hade, Sun Mara wa Kudirin Tinubu baya

  • Gwamnonin Arewa 19 bayyana cikakken goyon bayansu ga Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu kan matsalar tsaro
  • Sun bayyana cewa batun da Bola Tinubu ya yi na kafa 'yan sandan jihohi zai taka rawa wajen kakkabe matsalolin tsaro
  • Sai dai wasu daga cikin dattawan Arewa na ganin akwai abubuwan da ya kamata a yi kafin a tabbatar da wannan batu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa (NSGF) ta tabbatar da matsayinta na goyon bayan kafa rundunar ‘yan sandan jiha a Najeriya.

Gwamnonin na ganin hakan zai dakile tabarbarewar tsaro da ke addabar yankin Arewa da ma kasa baki ɗaya.

Gwamnonin Arewacin Najeriya sun goyi bayan Tinubu
Hoton Gwamnoni da Shugabannin Arewa yayin wani taro a Kaduna Hoto: @BMB1_Official
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta wallafa cewa wannan mataki ya biyo bayan aniyar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da kafa ‘yan sandan jiha a ƙasar.

Kara karanta wannan

Minista ya fadi yadda manufofin Tinubu su ka ceto albashin ma'aikata a jihohi 27

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin Arewa sun goyi bayan Tinubu

Daraktan yaɗa labarai na shugaban NSGF, kuma Gwamnan Jihar Gombe, Isma’ila Uba Misilli, ya tabbatar da goyon bayan gwamnonin.

Ya bayyana cewa gwamnonin Arewa 19 sun riga sun bayyana matsayarsu tun lokacin da suka gana da sarakunan gargajiya a Kaduna.

Ya ce:

“Gwamnonin Arewa sun amince da kafa ‘yan sandan jiha baki ɗayansu. Sun bayyana matsayarsu a ganawar da suka yi da shugabannin gargajiya a Kaduna."

Gwamnonin sun bukaci Majalisar Ƙasa da ta gaggauta aiwatar da duk wata doka da za ta ba da damar kafa rundunar ‘yan sandan jiha a Najeriya.

Sun bayyana yakinin cewa samar da yan sandan a karkashin ikon jihohi zai bayar da damar kakkabe kamarin da 'yan ta'adda su ka yi.

Ana fama da rashin tsaro a Arewa

Bukatar gwamnonin na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyi a yankin Arewa ke ci gaba da matsa lamba a kan matsalolin tsaro da suka yi kamari.

Kara karanta wannan

Bayan rasuwarsa, Tinubu ya fadi yanayin kasar da Buhari ya damka masa

Kungiyar ACF ta sha bayyana cewa yankin Arewa na cikin mawuyacin hali, kuma dole ne a fara daukar matakin kare jama'a.

Tinubu na da niyyar samar da yan sandan jihohi
Bola Tinubu, Shugaban Kasar Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ita ma kungiyar dattawan Arewa ta Northern Elders Forum (NEF) ta bukaci Shugaban Ƙasa da ya ayyana dokar ta baci a kan matsalar tsaro a Arewa.

Ana tsaka da wannan batu, gwamnonin Arewa maso Gabas daga jihohin Adamawa, Bauchi, Borno, Gombe, Taraba da Yobe, sun gana da Shugaba Tinubu a Abuja.

Sai dai ACF ta bukaci a tabbatar da cewa duk wani yunkuri na kafa ‘yan sandan jiha ya bi tsarin kundin tsarin mulki.

Haka kuma ta yi gargadin cewa kada a ba gwamnoni damar amfani da rundunar don murkushe ‘yan adawa.

Tinubu na son kafa 'yan sandan jihohi

A wani labarin, mun wallafa cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa kafa rundunar ‘yan sandan jiha a Najeriya tamkar wajibi ne.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi tawagar manyan ‘yan asalin Jihar Katsina karkashin Gwamna Dikko Umar Radda a fadar shugaban ƙasa.

Shugaba Tinubu ya nuna takaici kan yadda hare-haren ‘yan bindiga ke ƙaruwa a Jihar Katsina, lamarin da ya sa ya bada umarnin gaggawa ga jami’an tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng