'Yan Najeriya Za Su Biya Harajin N45 kan kowace Litar Fetur da Suka Saya daga 2026
- ’Yan Najeriya za su fara biyan sabon haraji daga 2026, inda kowace lita ta fetur za ta ƙara N45 idan farashinta ya tsaya a N900
- Sabuwar dokar haraji ta tanadi ƙarin 5% kan albarkatun man fetur, da nufin karkatar da 'yan ƙasar zuwa ga makamashi mai tsafta
- Sai dai, dokar ta lissafa wasu daga cikin kayayyakin mai da wannan harajin bai shafe su ba, saboda suna sahun makamashi mai tsafta
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - ’Yan Najeriya da ke sayen fetur za su biya ƙarin N45 kan kowace lita daga shekarar 2026 idan farashin litar ya ci gaba da kasancewa N900.
Wannan na zuwa ne sakamakon tanadin 5% a cikin Dokar Gudanar da Haraji ta 2025 da ya shafi kayayyakin mai da aka tace, domin ƙarfafa amfani da makamashi mai tsafta.

Source: Getty Images
An sanya harajin 5% kan man fetur
Ƙarin 5% kan kayayyakin mai da aka tace na cikin dokokin haraji hudu da Shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu a ranar 26 ga Yuni, 2025, kuma za a fara aiwatar da shi a Janairu 2026, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Manufofin dokar sun fi karkata ga kayayyakin man da ake samarwa ko tacewa a Najeriya.
Legit Hausa ta ruwaito cewa kayayyakin man fossil sun haɗa da fetur, dizal, kerosene, man jirgin sama da kuma gas din CNG, wadanda duk ake tacewa daga danyen mai, gas da kwal.
Sai dai kayayyakin da aka ware daga sabon harajin sun haɗa da makamashi mai tsafta ko wanda ake iya sabuntawa, kananzir, gas din girki da na CNG.
Abin da sabuwar dokar haraji ta ce
A cewar dokar, za a dora wannan ƙarin 5% kan dukkan “kayayyakin man fossil da aka dace” kuma za a lissafta shi bisa farashin da ake sayar da su, ba wai an kiyasce kudin ba ne.
Jaridar The Guardian ta rahoto cewa, dokar ta fayyace cewa ƙarin harajin zai shafi kowace iriyar “mu’amala da kayayyakin da aka tace” kamar saye da sayarwa.
Wani sashe na dokar ya ce:
“An dora harajin ƙarin 5% kan kayayyakin man fetur da aka samar ko aka tace a Najeriya, kuma za a cire harajin ne lokacin da aka gudanar da mu’amalar kudi.
“(1) Domin aiwatar da harajin, za a cire kudin mu’amala da kayayyakin, walau a lokacin samar da kaya, sayarwa, ko biyan kuɗi, duk dai wanda ya fara faruwa.
"(2) Za a lissafa harajin ne bisa farashin sayar da dukkan kayayyakin man fetur da cire harajin ya rataya kansa."

Source: Getty Images
Ranar da za a fara aiwatar da harajin
Sai dai, har yanzu ba a san takamaimai ranar da za a fara aiwatar da dokar ba, domin tana jiran sahalewar Ministan kudi da tsare-tsaren tattalin arziki, Wale Edun.
Dokar ta ce:
“Ta hanyar bayar da umarni a kafofin watsa labaran gwamnati, ministan na iya bayyana ranar da za a fara aiwatar da wannan haraji kan kayayyakin man fetur.”
Haka kuma, dokar ta bayyana cewa hukumar haraji ta kasa ce za ta rika tattara harajin a kowane wata tare da fitar da ƙa’idojin aiwatarwa.
Tinubu ya sanya hannu kan dokokin haraji
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannu kan sababbin kudirorin dokokin gyaran haraji huɗu da majalisa ta amince da su.
Waɗannan sababbin dokokin za su daidaita haraji, haɓaka kuɗaɗen shiga, da inganta yanayin kasuwanci, abin da Tinubu ya kira da 'sabon babi ga Najeriya.'
Dokokin sun haɗa da dokar haraji, dokar gudanar da haraji, dokar kafa hukumar haraji da kuma dokar kafa hukumar haɗin gwiwar haraji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


