An Fara Hayya Hayya a Neja bayan Hana Malamai Wa'azi sai da Lasisi
- Gwamnatin Jihar Neja ta bayyana cewa duk mai son yin wa’azi sai ya nemi lasisi a cikin wata biyu masu zuwa
- Shugaban hukumar kula da harkokin addinai ya ce dole ne a tantance malamai kafin a ba su izinin yin wa'azi
- Kungiyoyin addini da malamai sun rarrabu kan matakin gwamnatin, inda wasu ke ganin ya tauye ‘yancin addini
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Neja – Gwamnatin Jihar Neja ta dauki sabon mataki da ya haifar da muhawara a tsakanin malamai da shugabannin addinai.
Hakan na zuwa ne bayan ta sanar da cewa ba a yarda kowa ya yi wa’azi a cikin jihar ba sai bayan samun lasisi daga gwamnati.

Source: Facebook
Shugaban hukumar kula addini ta jihar ya bayyana dalilan da ya sa hukumar ta dauki matakin a wani bidiyo da shafin Tsalle Daya ya wallafa a Facebook.
Bayan sanarwar, kungiyoyin addinai da masana sun nuna ra’ayoyi mabambanta, inda wasu ke ganin matakin zai iya tabbatar da tsaro, yayin da wasu ke kallonsa a matsayin tauye ‘yanci.
Yadda za a yi rajistar malaman addini a Neja
Hukumar kula da harkokin addinai ta bayyana cewa an ba wa duk masu wa’azi wa’adin wata biyu su yi rajista kafin a ci gaba da ayyukansu.
Shugaban hukumar kula da harkokin addinai ta jihar, Umar Farooq, ya tabbatar da cewa gwamnati ta dauki wannan mataki domin tabbatar da zaman lafiya da guje wa tada fitina.
A cewarsa, duk wani malamin addini da yake son yin wa’azi dole ne ya ziyarci ofishin hukumar, ya cike fom, sannan ya tsaya gaban kwamitin da zai tantance shi kafin a ba shi lasisi.
Ya kara da cewa daga 4 ga Satumban 2025 zuwa wata biyu masu zuwa ne gwamnati ta bai wa malamai damar yin rajista kafin a fara aiwatar da dokar gaba daya.
Shugaban hukumar ya ce duk wanda ya yi wa'azi ba tare da lasisi ba bayan cikar wa'adin hukuma za ta dauki mataki a kansa saboda ya karya doka.
Ra’ayoyin malaman Musulunci a Neja
Punch ta wallafa cewa babban limamin jami’ar fasaha ta Minna (FUT Minna), Malam Bashir Yankuzo, ya ce wa’azi ibada ce da gwamnati ba ta da ikon hana shi gaba daya.
Ya ce abin da ya dace shi ne gwamnati ta sa ido kawai idan akwai malamai da ke amfani da wa’azi wajen tada rikici ko yin zagi, amma ba wai hana wa’azi gaba daya ba.
Haka zalika, wani malamin addini, Ustaz Hassan, ya nuna cewa ya kamata gwamnati ta kai wannan doka gaban majalisar dokoki domin ta samu ingantaccen tsari da ka’ida.
Ra’ayoyin Kiristoci da sauran ‘yan kasa
Sakataren kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) reshen Jihar Neja, Raphael Opawoye, ya ce kungiyar ba ta samu wata sanarwa kai tsaye daga gwamnati ba game da haramcin.
Ya ce idan har an tabbatar da matakin, za su fito da cikakkiyar matsaya bayan tattaunawa a cikin kungiyar.

Source: Facebook
A nasa bangaren, wani marubuci kuma malamin addini daga Minna, Uthman Siraja, ya yi Allah wadai da matakin, yana mai cewa hakan tauye ‘yanci ne na addini da ibada.

Kara karanta wannan
Ministan Buhari ya karyata zargin kashe N100bn don samar da jirgin saman Najeriya
Ya ce mafi dacewa shi ne gwamnati ta hukunta duk wani malami da aka samu yana tada zaune tsaye a cikin wa’azinsa maimakon hana wa’azi gaba daya.
Izala ta shirya wa'azi a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar Izala, karkashin Sheikh Abdullahi Bala Lau ta shirya gagurumin taro a jihar Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa bayan wa'azi da za ta yi, kungiyar za ta gabatar da wasu littattafan marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Nasir El-Rufa'i na cikin manyan bakin da kungiyar ta gayyata domin shaida taron da za ta yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

