Manyan Bukatu 4 da Gwamnonin Arewa Suka Gabatar wa Tinubu da Amsar da Ya ba Su

Manyan Bukatu 4 da Gwamnonin Arewa Suka Gabatar wa Tinubu da Amsar da Ya ba Su

  • Gwamnonin Arewa maso Gabas sun mika wa Shugaba Bola Tinubu jerin bukatu hudu da suka shafi tsaro da ababen more rayuwa
  • Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ne ya jagoranci gwamnonin a ziyarar da suka kai wa Tinubu a fadar shugaban kasa, Abuja
  • Manyan bukatun da gwamnonin suka gabatar sun haɗa da ci gaba da kai hare-haren sojoji, da kuma kammala wasu manyan ayyuka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Gwamnonin Arewa maso Gabas sun gabatar wa shugaba Bola Ahmed Tinubu jerin bukatu hudu da suka shafi tsaro da ababen more rayuwa.

Mun ruwaito cewa, gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ne ya jagoranci gwamnonin a ganawar da suka yi da Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Gwamnonin Arewa maso Gabas sun gabatar da bukatu hudu ga Shugaba Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu ya gana da gwamnonin Arewa maso Gabas a fadar shugaban kasa, Abuja. Hoto: @TarabaFacts
Source: Twitter

A yayin ganawar, sun jaddada matsalolin da suke fuskanta a yankin, ciki har da rashin tsaro, da rashin ci gaban yankin, a cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya fadi yadda 'yan adawa suka saka APC a gaba da fara kamfen

Bukatu 4 da gwamnoni suka gabatar wa Tinubu

Gwamna Zulum, wanda ya yi magana a madadin takwarorinsa, ya ce gwamnonin sun kuduri aniyar hada kai da shugaban kasa wajen samar da shugabanci nagari.

Gwamnan ya jaddada bukatar samun goyon baya daga gwamnatin tarayya don tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Ya ce gwamnonin "sun hadu gaba daya" don mara wa shirin Tinubu na Renewed Hope baya, kuma suna da yakinin cewa hadin gwiwar zai kawo sauyi a yankin Arewa maso Gabas.

Manyan bukatun da suka gabatar sun haɗa da:

  1. Ci gaba da ayyukan soji a tafkin Chadi da dajin Sambisa.
  2. Samar da kudade ga dakarun hadin gwiwa na kasa da kasa (MJTF).
  3. Ci gaba da hako man fetur a rijiyoyin Kolmani da na tafkin Chadi.
  4. Kammala manyan ayyukan titina, kamar titin Kano–Maiduguri, titin dogo na Port Harcourt–Jos–Bauchi–Maiduguri, da kuma wasu titunan da ke tsakanin jihohi, ciki har da Bama–Mubi–Yola, Wukari–Jalingo–Yola, Bauchi–Gombe–Biu–Damaturu, da Damaturu–Geidam.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun gana da Tinubu a Abuja, sun roƙi manyan alfarma 2

Martanin Tinubu ga bukatun gwamnonin Arewa

Da yake mayar da martani, Shugaba Tinubu ya yabawa kokarin gwamnonin musamman wajen amfani da C-JTF tare da sauran jami’an tsaro a yaki da 'yan ta'adda.

Shugaba Bola Tinubu ya ce zai duba yiwuwar kafa 'yan sandan jihohi don yaki da matsalar tsaro.
Gwamna Babagana Zulum yana gaisa wa da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa, Abuja. Hoto: @abdullahayofel
Source: Twitter

Jaridar This Day ta rahoto Tinubu ya kuma yi alkawarin binciko yiwuwar samar da 'yan sandan jihohi ta hanyar tattaunawa da majalisar tarayya, don inganta tsaro a jihohi.

Tinubu ya ce:

“Idan muka cire siyasa a gefe, za mu iya aiki tare da majalisar tarayya don kawar da matsalolin siyasa daga 'yan sandan jiha. Wannan zai samar da karin kariya ga al'umma.”

Shugaban kasar ya kuma baiwa gwamnonin tabbacin cewa, babban burinsa shi ne samar da tsaro, ci gaba, da shugabanci nagari a Najeriya.

Ya kara da cewa hadin kai tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnonin zai taimaka wajen gina Najeriya, tare da samawa al'umma ci gaban da suke mafarki.

Gwamnonin Arewa sun hango matsala a 2026

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar gwamnonin Arewa maso Gabas ta ce akwai yiwuwar a samu tsadar kayan aikin noma, wanda zai jawo tsadar abinci a 2026.

Kara karanta wannan

"Akwai sauran gurabe": Tinubu ya kwantar da hankalin 'yan kungiyar Buhari

Gwamnonin sun nuna wannan fargabar ne a taronsu na 12 da aka gudanar a Jalingo, jihar Taraba, kamar yadda mai masaukin baki, Gwamna Agbu Kefas ya sanar.

Haka kuma, gwamnonin sun nuna damuwa game da yiwuwar ambaliya a yankin, bisa rahotannin da hukumomin kula da hasashen yanayi suka fitar na baya-bayan nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com