Minista Ya Fadi Yadda Manufofin Tinubu Su ka Ceto Albashin Ma'aikata a Jihohi 27
- Ministan bayanai, Mohammed Idris ya ce gyare-gyaren Shugaba Bola Tinubu sun kawo ƙarshen matsalar biyan albashi a jihohi 27
- Ya bayyana cewa cire tallafin mai ya buɗe sababbin hanyoyin samun kuɗi da ke ba gwamnoni damar kaddamar da ayyuka ga jama’a
- Ya ƙara da cewa a baya kashi 97 cikin 100 na kuɗin shiga na tarayya ana kashe su wajen biyan bashi, abin da ya jefa jihohi cikin wahala
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana cewa manufofin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar suna amfani.
Ya bayyana cewa daga cikin yadda suka taimaka wa kasar nan shi ne kawo ƙarshen dogon rikicin biyan albashi a jihohi 27 daga cikin 36 na Najeriya.

Kara karanta wannan
Ministan Buhari ya karyata zargin kashe N100bn don samar da jirgin saman Najeriya

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Mohammed Idris ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Laraba lokacin da kwamishinonin yada labaran jihohi suka kai masa ziyarar ban-girma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Minista ya fadi amfanin manufofin Tinubu
TVC News ta ruwaito Ministan ya ce shirye-shiryen da shugaban kasa ke aiwatarwa ba na siyasa ba ne, sai dai don kawo ci gaba ba tare da nuna bambanci ba.
Ya ce:
“Ban taɓa ganin inda akwai aiki a wani jiha, shugaban kasa ya ƙi yi saboda gwamnan jihar ba na jam’iyyar APC ba ne."
Mohammed Idris ya bayyana cewa cire tallafin mai ya kawo damar samun karin kudin shiga, abin da ya bai wa gwamnoni damar kaddamar da muhimman ayyuka da jama’a ke amfana da su kai tsaye.

Source: Facebook
Ya ce:
“Cire tallafin mai ya ba shugabanninku damar fara ayyuka, suna kawo wa jama’a ribar daga dimokuradiyya."
Gwamnoni na iya biyan albashi a mulkin Tinubu

Kara karanta wannan
Tinubu ya amsa kira kan kirkirar 'yan sandan jihohi, ya gano sirrin magance ta'addanci
Mohammed Idris ya ƙara da cewa kafin Tinubu ya hau mulki, ana kashe 97% na kuɗin shiga na tarayya a wajen biyan bashi, abin da ya bar jihohi cikin ƙalubalen biyan albashi.
Ya ce gyare-gyaren da shugaban kasa ya aiwatar sun dawo da kwanciyar hankali a harkar kuɗi tare da buɗe hanyoyi na ci gaban ƙasa.
Ministan ya sanar da cewa ma’aikatarsa za ta kai ziyara zuwa jihohin Kudu maso Kudu da Arewa maso Gabas don duba ayyuka tare da jin ra’ayin jama’a a kai tsaye.
Haka kuma ya shawarci kwamishinonin su ci gaba da amfani da hukumomin yada labarai irin su Hukumar Wayar da Kan Jama’a (NOA), gidan talabijin NTA, tashoshin Voice of Nigeria da FRCN wajen yaɗa shirye-shirye ga jama’a.
A nasa jawabin, kwamishinan bayanai na Borno kuma shugaban taron kwamishinonin, Usman Tar, ya ce za su tallata ayyukan kasa ba tare da nuna bambancin jam'iyya ba.
'Dan majalisa ya shawarci Tinubu
A wani labarin, mun wallafa cewa Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, dan majalisar tarayya mai wakiltar Kiru/Bebeji a jihar Kano karkashin jam’iyyar NNPP, ya mika shawara ga Bola Tinubu.
Ya bayyana cew canza Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima na iya zama kuskure a siyasar APC kamar yadda aka samu matsala a shekarar 2023.
Ya ce akwai bukatar Bola Ahmed Tinubu ya yi taka tsantsan da mutanen da ke ba shi shawarar ya sauya Kashim Shettima saboda illar hakan ga siyasarsa a zabe mai zuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
