'Rashin Adalci ne,' Sanata Ndume Ya ce ana Mayar da Harin Boko Haram Batun Addini
- Sanata Ali Muhammad Ndume ya gargadi a guji bayyana cewa Boko Haram na kashe kiristoci ne kawai a yankin Arewa maso Gabas
- Ya ce da musulmai da kiristoci, dukkannisu na fuskantar hare-haren ta’addanci a yankin, musamman a jihar Borno da aka saba kai hari
- Ndume ya soki rahotannin da ke nuna cewa kiristoci kaɗai ake kai wa hari, yana mai kiran hakan ba daidai ba kuma zai iya haddasa fitina
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya yi gargaɗi kan yin amfani da bambancin addini wajen rarrabe waɗanda ke fuskantar hare-haren Boko Haram.
Ya ce irin wannan salo zai iya haddasa ƙarin rikici da kuma lalata haɗin kan ƙasa a lokacin da Boko Haram ke ci gaba da kai hari babu nuna wariya..

Source: Twitter
Jaridar Leadership ta wallafa cewa Sanatan ya fitar da wannan sanarwa ne a ranar Alhamis a birnin Abuja
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar na zuwa ne bayan hare-haren da aka kai a ƙauyen Ngoshe na ƙaramar hukumar Gwoza da kuma Mussa a Askira-Uba – dukkanninsu a jihar Borno.
Boko Haram ta kai hari a jihar Borno
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa a hare-haren daban-daban da aka kai, an kashe manoma musulmai guda biyar a Ngoshe a ranar Asabar.
Sannan an kashe kiristoci uku mazauna Mussa ranar Lahadi. Rahotanni kuma sun tabbatar da cewa ‘yan ta’addan sun ƙona gidaje da dama a lokacin hare-haren.
A martaninsa, Ndume ya bayyana takaicinsa kan wani rahoton kafar watsa labarai na intanet da ya yi ikirarin cewa dukkannin mutanen da aka kashe kiristoci ne.

Source: Original
Ya ce:
“Abin a karyata ne kuma rashin da’a ga kowace jarida ta rika yada labarin cewa kiristoci kaɗai ake kai wa hari a Borno ko Arewa maso Gabas baki ɗaya.”

Kara karanta wannan
Ministan Buhari ya karyata zargin kashe N100bn don samar da jirgin saman Najeriya
Ndume: ''Yan Boko Haram na barna'
Sanata Ali Ndume ya jaddada cewa masu kisan gilla ba sa kallon addini ko kabila kadin du aiwatar d mugun nufinsu a kan bayin Allah.
Sanata Ndume ya ce:
“Wajibi ne mu guji irin wannan nuna bambanci saboda zai iya jawo ƙiyayya, har ma ya rage kwarin gwiwar sojojinmu da ke aiki dare da rana domin kawar da wannan ƙungiya ta’addanci."
Ndume ya nanata cewa dukkannin al’ummar yankin, walau musulmi ko kirista, daga kowane yanki na fuskantar barazana.
Ya bayyana cewa waɗanda ke mutuwa a rikicin ‘yan ta’adda mutane ne da burinsu kawai shi ne su rayu lafiya da kuma yin noma.
Ya ce:
“Mutanenmu, waɗanda burinsu shi ne zaman lafiya da samun abincin yau da kullum, su ne ke ci gaba da fada wa komar 'yan ta'adda. Waɗannan maza da mata sun cancanci su rayu."
Boko Haram: Ndume ya yabi sojojin Najeriya
A baya, kun ji cewa Sanata Mohammed Ali Ndume, ya nuna gamsuwarsa da jarumtar dakarun sojoji, mafarauta da ƴan sa-kai na CJTF wajen fatattakar mayakan Boko Haram.
A wani biki da aka shirya, Ndume ya bayar da kyautar shanu guda uku da kuma Naira miliyan biyu domin a yi murnar nasarar da aka samu a kan ‘yan ta’addan.
Rahotanni sun bayyana cewa za a bayar da shanu biyu ga mafarauta da CJTF na Izge da Yamtake, yayin da ɗaya za a bayar ga dakarun gwamnati da suka yi fice wajen kare jama’a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

