Hatsarin Jirgi Ya Rutsa da Mutane kusan 100 a Hanyar zuwa Gidan Gaisuwa, An Rasa Rayuka
- Hukumar NSEMA ta tabbatar sa faruwar wani hatsarin jirgin ruwa a yankin karamar hukumar Borgu ta jihar Neja
- Jirgin na dauke da mutane kusan 100, wanda aka gano cewa su na hanyar zuwa gaisuwar wata rasuwa da aka yi ne a yankin
- Shugaban NSEMA, Abdullahi Baba Arah ya ce wadanda ke cikin jirgin sun karya dokar da gwamnatin Neja ta sanya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Niger - Rahotanni sun tabbatar da cewa an kara samun hatsarin jirgin ruwa da ya hallaka gomman mutane a yankin karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.
Hatsarin jirgin ruwan, wanda ya dauko mutane kusan 100, ya yi sanadiyyar mutuwar fasinjoji 29, yayin da har yanzu ba a ga mutane biyu daga ciki ba.

Source: Getty Images
Jaridar Leadership ta tattaro cewa jami'an ceto da sauran mutanen da suka kai dauki sun samu nasarar ceto mutum 50 da da ransu a hatsarin wanda ya auku a Borgu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda jirgin ruwa ya nutse da mutane 90
Bayanai sun nuna cewa hatsarin ya faru ne a kauyen Gausawa, da ke yankin Malale, inda aka tabbatar cewa mutum 90 ne ke cikin jirgin lokacin da hatsarin ya auku.
An gano cewa jirgin ya tashi ne daga Tugan Sule da ke cikin gundumar Shagunu, dauke da fasinjoji mafi yawansu mata da yara, da nufin zuwa Dugga domin yin gaisuwar rasuwa.
Wani ganau ya bayyana cewa jirgin ya cika makil da fasinjoji tun daga lokacin da ya bar Tugan Sule, sai da ya kusa isa Gausawa, sannan ya kife nan take.
Me ya haddasa hatsarin jirgin a Neja?
Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA), Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Abdullahi Baba ya ce:
“Mun samu rahoton hatsarin jirgin ruwa a wani kauye mai suna Gausawa da ke yankin Malale a karamar hukumar Borgu.
“Bisa ga rahoton jami’inmu da ke jagorantar aikin bincike da ceto, jirgin ya tashi daga garin Tugan Sule da fasinjoji 90 ciki har da mata da yara, inda suka nufi Dugga don yin gaisuwar rasuwa.”
Shugaban NSEMA ya bayyana cewa dalilan hatsarin sun haɗa da cika jirgin fiye da kima da kuma bugun wata bishiya da ke ƙarƙashin ruwa.

Source: Twitter
NSEMA ta tabbatar da ceto mutane 50 a raye
Haka kuma, ya tabbatar cewa babu wanda ya sanya rigar ruwa saga cikin fasinjojin jirgin duk da dokar gwamnati da ta tilasta hakan a jihar, in ji Punch.
Ya ƙara da cewa, an riga an ceto mutane 50 da ransu, sannan an ciro gawarwakin mutum 29, yayin da ake cigaba da aikin bincike don gano sauran mutum biyu da suka ɓace.
Jirgin ruwa ya nutse da mutane a Sakkwato
A wani labarin, kun ji cewa jirgin ruwa dauke da mutane da dama ya kife a yankin karamar hukumar Shagari ta jihar Sakkwato.
Rahotanni sun tabbatar da cewa jirgin ruwan wanda ke cike da fasinjoji har ya wuce kima, ya nutse a ruwa lamarin da ya jawo asarar rayuka da kuma bacewar wasu.
Wasu shaidu sun ce jirgin da ya yi hatsarin ya dauko maza, mata da yara fiye da ƙima kafin kifewarsa a tsakiyar ruwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

