Tinubu Ya Amsa Kira kan Kirkirar 'Yan Sandan Jihohi, Ya Gano Sirrin Magance Ta'addanci
- Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce a yadda lamarin tsaron kasar nan ke tafiya, ba za a iya watsi da batun samar da 'yan sandan jihohi ba
- Ya ce a yanzu haka ya fara nazari a kan al'amarin da zummar gano hanyar da ta dace wajen aiwatar da tsarin domin karfafa taron kasar nan
- Bola Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da Najeriya, musamman jihohin da ke Arewacin kasar nan ke fama da matsalar 'yan ta'adda
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa samar da rundunar ‘yan sanda ta jihohi abu ne da ba za a iya guje masa ba.
Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin da ya karɓi tawagar manyan ‘yan asalin Jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Dikko Radda a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa shugaban ƙasan ya kuma ba jami’an tsaro umarni da su sake nazari kan yadda suke aiki a Katsina, sakamakon ƙaruwa da ta’addancin ‘yan bindiga a jihar.
Tinubu ya yi takaicin karuwar hare-hare a Katsina
Independent Newspaper ta wallafa cewa Tinubu ya ce gwamnatin tarayya za ta tura karin makaman zamani da na’urorin leƙen asiri a jihar domin ƙarfafa tsaro.
Shugaba Tinubu ya kara da cewa gwamnatin tarayya tana duba yiwuwar ƙara inganta masu gadin daji da aka tura Katsina domin su taimaka wajen dakile ayyukan ta’addanci.
Ya ce:
“Za mu iya magance kalubalen tsaro da muke fuskanta. Tabbas, muna da iyakokin da ke da rauni. Amma dole mu gyara matsalar, kuma muna kokarin hakan da karfinmu."
“Na bayar da umarni a yau cewa dukkannin jami’an tsaro su ƙara ƙaimi su kuma sake duba dabarunsu. Mun amince da sayo karin jiragen leƙen asiri.”
Shugaba Tinubu ya ba jami'an tsaro umarni
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kuma umarci jami’an tsaro da su rika ba shi rahoton tsaro kullum daga Katsina.
Ya ce:
“Ina sake nazari kan fannoni daban-daban na tsaro; dole ne in samar da rundunar ‘yan sanda ta jihohi. Muna duba batun."
“Za yi nasara a kan matsalar rashin tsaro. Dole ne mu kare ‘ya’yanmu, al’ummarmu, abincinmu, wuraren ibada da wuraren hutu. Ba za su iya razana mu ba.”

Source: Twitter
A ranar 15 ga Fabrairu, 2024, gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti domin binciko yiwuwar samar da rundunar ‘yan sanda ta jihohi.
Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa shugaban ƙasa da gwamnoni sun amince da hanyoyin aiwatar da tsarin.
Tun a 2023 aka ji cewa gwamnonin jihohin da ke Arewa suna goyon bayan wannan yunkuri.
Jigon APC ya ce Tinubu zai zarce
A wani labarin, mun wallafa cewa jagora a jam'iyya mai mulki ta APC, Farouk Adamu Aliyu ta bayyana cewa babu abin da zai kawo cikas ga Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin baiwa jihar Legas fifiko wajen ayyukan raya kasa
Ya yi wannan kurin ne a yayin da yake amsa tambayoyi game da salon mulkin shugaban ƙasa da makomar jam’iyya a babban zaɓen 2027 da ke tunkaro kasar nan.
Farouk Adamu Aliyu ya nuna cewa APC na da tabbacin ci gaba da rike madafun iko saboda kwarewar shugabancin Tinubu, da rawar da ya taka wajen gyaran tsarin tattalin arziki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

