'Adawa da Gwamna': Ƴan Daba Sun Zare Wuƙaƙe, Sun Tarwatsa Taron Tsaro a Katsina
- Taron tsaro da kungiyar KSCI ta shirya ya gamu da cikas bayan wasu da ake zargi da ’yan daba ne suka farmaki mutane da wukake
- Rikicin ya tashi ne bayan Dr Bashir Kurfi ya bayyana yadda ’yan bindiga suka mamaye garuruwa da makarantu a jihar Katsina
- 'Yan daban sun kai hari kan ’yan jarida, wasu ma sun fito da makamai, yayin da suka ce ba za su bari a soki gwamnatin Dikko Radda ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Katsina – Wasu da ake zargi da ’yan daba ne sun tarwatsa wani taron tsaro a jihar Katsina a ranar Talata, tare da kai hari ga mahalarta taron da ma ’yan jarida.
Taron, wanda kungiyar ci gaban tsaron Katsina (KSCI) ta shirya, ya haɗa masana tsaro, jami’an soja da ’yan sanda da suka yi ritaya, da malamai, da shugabanni, don tattaunawa kan matsalar tsaron jihar.

Source: Original
Katsina: 'Yan daba sun hargitsa taron tsaro
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, an fara taron cikin lumana, har zuwa lokacin da Dr Bashir Kurfi, wanda ya shirya taron ya fara jawabi kan halin da jihar ke ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dr. Bashir ya bayyana cewa hare-haren 'yan bindiga ya ruguza wasu kananan hukumomi a Katsina, inda harkokin noma da kiwo suka tsaya cak, kuma an rufe makarantu, ko kuma ’yan bindigar sun mamaye su.
Sai wani mutum ya katse maganarsa da cewar gwamnati na bakin kokarinta, kuma bai amince a ci gaba da abin da ya kira 'suka da adawa ga gwamnati' ba.
Katsina: Hankula sun tashi a taron tsaro
Bayan haka, wasu da dama daga cikin wadanda ake zargin 'yan daba ne suka tashi suka fara hayaniya, suna yin wurgi da kujeru tare da kai hari ga ’yan jarida.
Shaidun gani da ido sun ce wasu daga cikin mutanen da suka hargitsa taron sun fito da wukake, suna barazanar farmakar duk wanda ya zama “makiyi ga gwamnati”.
Wani mahalarcin taron ya bayyana cewa, ’yan daba sun dade a wajen taron, a ciki da wajen wurin zama, suna jiran damar tada rikici.
Masu shirya taron sun mayar da martani
Daga bisani, Dr Kurfi da abokan aikinsa sun yi taron manema labarai a wani wurin daban, inda suka ce za su ci gaba da shirya taro kan yanayin tsaro a Katsina.
Sun ce abin mamaki ne ganin gwamnati ta yi irin wannan abu, duk da cewa an sanar da ita tun daga tarurrukan baya da aka yi a Abuja da Kaduna.
Dr Kurfi ya yi zargin cewa shugabannin kananan hukumomi na da hannu a hargitsin, yana mai cewa an ga daya daga cikinsu yana ba ’yan daba kudi.

Source: Facebook
Martanin gwamnatin Katsina kan taron tsaro
Da aka tuntubi gwamnatin jihar Katsina, kwamishinan watsa labarai da al’adu, Dr Bala Salisu Zango, ya ce bai san da taron ba balle rikicin da ya faru.
Amma ba a samu amsar sakon da aka tura ga daraktan yada labarai na gwamna, Maiwada Dammallam ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Kara karanta wannan
'Yan daba sun tarwatsa taron ƴan adawa da El Rufa'i ya halarta a Kaduna, an ji raunuka
Radda, kusoshin Katsina sun gana da Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya ba sojoji da sauran jami'an tsaro umarnin tsaurara sa ido kan hare-haren 'yan bindiga a Katsina.
Tinubu ya nuna takaicinsa kan yadda matsalar tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a Katsina, yana mai cewa, za a sake fasalin yadda ake yakar 'yan ta'adda a jihar.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da wata tawaga daga jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Dikko Umaru Radda, ta gana da shi a fadar shugaban kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

