Ana Wata ga Wata: Shugabannin NTA da Tinubu Ya Kora a Agusta Sun Dawo Bakin Aiki
- Bola Tinubu ya dawo da Salihu Dembos a matsayin shugaban NTA domin kammala wa’adinsa na shekaru uku da ya fara a 2023
- Haka zalika, shugaban kasar ya dawo da Ayo Adewuyi kan matsayinsa na Daraktan labarai na NTA, inda wa’adinsa zai kare a 2027
- Bayan daukar wannan mataki, fadar shugaban kasa ta fadi makomar sababbin shugabannin NTA da Tinubu ya nada a Agusta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin dawo da Salihu Abdullahi Dembos a matsayin shugaban Gidan Talabijin na Ƙasa (NTA).
Haka kuma, shugaban ya dawo da Ayo Adewuyi a matsayin daraktan labarai na NTA domin ya kammala wa’adinsa da zai kare a shekarar 2027.

Source: Twitter
Tinubu ya dawo da tsoffin shugabannin NTA
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya fitar a shafinsa na X a ranar Talata, 2 ga Satumba 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce:
“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin dawo da Mr Salihu Abdullahi Dembos, kan kujerarsa ta shugaban Gidan Talabijin na Ƙasa (NTA).
“Shugaban kasar ya kuma bayar da umarnin dawo da Mr Ayo Adewuyi, kan kujerarsa ta daraktan labarai, domin ya kammala wa’adinsa na shekaru uku, wanda zai kare 2027.”
Janye nadin sababbin shugabannin NTA
Sanarwar ta ƙara da cewa wannan umarni “ya soke sababbin nade-naden da aka sanar a baya” ciki har da na shugaba, Daraktan labarai, Daraktan kasuwanci, da kuma Babban darekta.
Tinubu ya yi sababbin nade-naden ne a watan Agusta, 2025, inda aka nada Rotimi Richard Pedro a matsayin shugaban NTA don maye gurbin Salihu Dembos.
Haka kuma, a lokacin ne aka nada Stella Din-Jacob a matsayin daraktar labarai, Karimah Bello ta zama daraktar kasuwanci, yayin da Sophia Essahmed ya samu mukamin MD na NTA.
Nadin Pedro ya samu yabo daga masana, inda BOAPR ta bayyana PEdro a matsayin “jajurtacce, kwararre kuma mai hangen nesa," inji rahoton Vangaurd.
NTA: Wasu sun ga samu sun ga rashi
Haka nan, ƙungiyoyin mata ciki har da NAWOJ ta reshen Abuja sun yaba da nadin Din Jacob, inda suka bayyana hakan a matsayin “nasara ga mata a masana’antar yada labarai.”
Amma da wannan sabon umarni, Dembos zai ci gaba da jagorantar NTA har zuwa shekarar 2026, yayin da Adewuyi zai rike mukaminsa har zuwa 2027.
Sanarwar ba ta bayyana dalilin wannan sauyi ba, amma ta tabbatar cewa shugaban kasa ya soke sabbin nade-nade kuma ya dawo da tsoffin shugabanni bakin aikinsu.
Tinubu ya nada sababbin daraktoci a NTA
A wani labarin, mun ruwaito yadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sababbin daraktoci shida a gidan talabin na kasa, watau NTA.
Bayo Onanuga, mai magana da yawun Tinubu, ya ce daraktocin da aka nada sun hada da Ibrahim Aliyu (sashen ayyuka na musamman) da Muhammed Mustapha (sashen gudanarwa da horarwa.
Sanarwar Onanuga, ta kuma bayyana cewa, Bola Tinubu ya amince da sake naɗin Ayo Adewuyi a matsayin babban daraktan sashen labarai na NTA.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

