Likitoci Sun Shata wa Gwamnatin Tinubu Layi, Za Su Dauki Mataki a cikin Kwanaki 10

Likitoci Sun Shata wa Gwamnatin Tinubu Layi, Za Su Dauki Mataki a cikin Kwanaki 10

  • Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta NARD ta gargadi gwamnatin tarayya da na ta wasu jihohin kasar nan
  • Kungiyar ta ce tun a baya da aka shiga yarjejeniya da gwamnati, an yi biris da matsayar da aka cimma don inganta aiki
  • Bayan wani taro da kungiyar ta gudanar a ranar Lahadi, ta fitar da sanarwa a kan mataki na gaba da za ta dauka bayan kwana 10

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT AbujaƘungiyar likitoci masu neman kwarewa ta NARD ta zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da yi wa bukatunsu rikon sakainar kashi.

Kungiyar ta rufe ido, inda ta baiwa gwamnatin tarayya da hukumomin da abin ya shafa wa’adin kwanaki 10 domin biyan bukatun jin daɗin ma’aikatanta.

Kara karanta wannan

Bayan gargadin NEMA, Ambaliya ta afka wa dubban mutane a Adamawa

NARDta gargadi gwamnatin Bola Tinubu
Hoton Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Ajuri Ngalela
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa wannan na dauke a cikin wata sanarwa da Shugaban NARD na kasa, Dakta Tope Osundara; Sakatare Janar, Dakta Oluwasola Odunbaku su ka sa wa hannu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar NARD ta gargadi gwamnatin Tinubu

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa kungiyar ta bayyana cewa za ta dauki mataki idan gwamnati ta shafe wadannan kwanaki ba a biya bukatun 'ya'yanta ba.

A cikin sanarwar da kungiyar ta fitar, NARD ta ce za ta tsunduma wani babban yajin aiki da zai girgiza bangaren lafiya bayan kwanaki 10.

Ta ce matakin ya biyo bayan taron gaggawa na majalisar zartarwa ta ƙasa (E-NEC) da aka gudanar ta yanar gizo ranar Lahadi.

NARD ta tunatar da cewa tun watan Yuli ta baiwa gwamnati wa’adin makonni uku, amma saboda son zaman lafiya, ta tsawaita shi da wasu makonni uku amma shiru.

NARD ta zargi gwamnati da watsi da ita

Sanarwar ta nuna damuwa kan yadda aka gaza biyan kuɗin horon likitoci masu neman kwarewa na shekarar 2025 ga yawancin likitoci.

Kara karanta wannan

MURIC ta kausasa harshe kan kisan matar da ake zargi da kalaman batanci a Neja

Haka kuma ta bayyana cewa an ki biyan bashin watanni biyar na karin albashin CONMESS (25%/35%) tare da sauran tsofaffin hakkokinsu.

Haka nan, ƙungiyar ta yi tir da rage darajar takardun 'ya'yan kungiyar da daga West African Colleges of Physicians and Surgeons da hukumar MDCN ta yi.

NARD ta kuma soki rashin biyan kuɗin kayan aiki na shekarar 2024 da wasu jihohi suka yi, musamman gwamnatin Kaduna da ta gaza bin yarjejeniyar da ta sanya hannu da ARD Kaduna da Asibitin Barau Dikko.

NARD ta zargi gwamnatoci da watsi da bukatunsu
Shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ta kuma zargi gwamnatin Oyo da kin magance matsalolin da asibitin LAUTECH Ogbomosho ke fuskanta, duk da yajin aikin da ake yi a asibitin.

Sai dai ƙungiyar ta yaba wa gwamnonin jihohin da suka riga suka biya kuɗin MRTF na 2025, tana mai cewa hakan alama ce ta kishin jin daɗin ma’aikata.

NARD ta nemi biyan dukkannin hakkokin da ake bin ta, dawo da martabar takardun karatun ƙwararru, da kuma warware matsalolin likitoci a jihohin Kaduna da Oyo.

NARD ta mika bukata ga gwamnati

Kara karanta wannan

Ribadu ya karyata El-Rufai, ya zarge shi da siyasantar da matsalar tsaro

A shekarun baya, kun ji cewa kungiyar NARD ta bayyana buƙatarta ga Shugaban Najeriya na baya, Muhammadu Buhari na cewa a sallami wasu ministoci da shugabannin ma’aikatun lafiya.

Shugaban ƙungiyar, Uyilawa Okhuaihesuyi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa Litinin, 9 ga Agusta, 2021, inda ya nanata cewa duk wanda ya gaza sauke nauyin da ke kansa, a sauke shi.

Ya ce, ya kamata a sallame su Ministan kwadago Chris Ngige, Ministan lafiya Osagie Ehanire da Shugaban MDCN, Tajuddeen Sanusi, saboda rashin iya sauke nauyin da aka ɗora musu

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng