Yajin Aikin NARD: Kungiyar Likitoci Ta Bukaci Shugaba Buhari Ya Sallami Wasu Ministocinsa

Yajin Aikin NARD: Kungiyar Likitoci Ta Bukaci Shugaba Buhari Ya Sallami Wasu Ministocinsa

  • Kungiyar likitoci masu neman kwarewa (NARD) ta bukaci a sallami ministoci biyu daga aikinsu
  • Shugaban ƙungiyar, Uyilawa Okhuaihesuyi, shine ya bayyana haka, yace babu amfanin barin wanda ba zai iya aikinsa ba
  • Yace kungiyarsu ba zata janye yajin aikin da take ba har sai an biya musu bukatunsu

Abuja - Shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewa (NARD), Uyilawa Okhuaihesuyi, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta sallami duk wanda ke da hannu a yajin aikin da likitoci ke yi a kasar nan.

Okhuaihesuyi yace ya kamata a sallami ministan kwadugo, Chris Ngige, ministan lafiya, Osagie Ehanire, da kuma shugaban MDCN, Tajuddeen Sanusi, matukar ba zasu iya sauke nauyin dake kansu ba.

The Cable ta ruwaito cewa a ranar 2 ga watan Agusta, likitocin suka tsunduma yajin aiki bisa rashin biyansu albashi, da wasu alawus da dai sauransu.

Ministan kwadugo, Dakta Chris Ngige
Yajin Aikin NARD: Kungiyar Likitoci Ta Bukaci Shugaba Buhari Ya Sallami Wasu Ministocinsa Hoto: thisdaylive.com
Asali: UGC

Gwamnati ta biya wa likitoci bukatunsu

Da yake jawabi game da lamarin, ministan kwadugo, Chris Ngige, yace gwamnati zata aiwatar da ba aiki ba biyan albashi a kan likitocin saboda an biya musu bukatunsu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta fusata, ta ce duk likitan da ya shiga yajin aiki ba shi ba albashi

Da yake martani kan maganar ministan yayin wata fira da Channels tv, shugaban NARD yace ba zai yuwu ministan ya yaudaresu ba.

Ya kuma kara da cewa ya kamata jami'an gwamnati dake da hannu a wannan yajin aikin su yi murabus ko a sallamesu.

Dagaske gwamnati zata maye gurbinsu?

Okhuaihesuyi ya ƙalubalanci ministan game da wata barazana da ya yi wa likitocin cewa gwamnati zata iya maye gurbinsu da wasu likitocin na daban.

A jawabinsa, shugaban NARD yace:

"Idan kanason aiwatar da dokar ba aiki ba biya, to ina tunanin sai ka nemo likitoci 16,000 da zasu maye gurabinmu."
"Ina kira ga yan Najeriya su faɗa musu cewa duk masu hannu a wannan yajin aikin saboda kin yin aikinsu yadda ya kamata su yi murabus ko a sallamesu daga mukamansu."
"Saboda matukar ba zaka iya aikin da aka ɗora maka ba, babu amfanin kasancewarka a wannan ofis ɗin."

Kara karanta wannan

Ngige: Na ja kunnen 'ya'yana likitoci da kada su shiga yajin aikin nan na rashin hankali

Su waye ke da hannu a yajin aikin?

Da aka tambayeshi, su waye suka jawo wannan yajin aikin, Shugaban NARD ya bayyana cewa:

"Ma'aikatar lafiya, ma'aikatar kwadugo (yana nufin ministoci), shugaban MDCN, waɗannan sune suka sanya muka shiga wannan yajin aikin."
"Ya kamata a ɗauki mataki a akansu idan ba zasu iya sauke nauyin da aka ɗora musu ba. Zasu iya aiwatar da dokar ba aiki ba biya, mu kuma zamu jure."

Yaushe zaku koma aiki?

Hakanan da aka tambaye shi ko kungiyarsu zata janye yajin aikin, yace:

"Ba zamu janye ba, mun yanke hukunci kuma mambobin kungiyarmu suna son a cigaba a haka har sai mun cimma bukatar mu."

A wani labarin kuma Gwamna Zulum Ya Bayyana Yadda Yake Farin Ciki da Yan Boko Haram/ISWAP Suke Tuba a Borno

Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, ya nuna jin dadinsa da yadda yan ta'adda ke tuba su mika makamansu.

Kara karanta wannan

Martanin 'yan Najeriya ga IBB kan tsokacin rashawa da tayi katutu a gwamnatin Buhari

Kwamishinan yaɗa labaran jihar Borno, Abba-Jato, shine ya bayyana haka jim kaɗan bayan fitowa daga taron tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262