COVID-19: Kungiyar NARD za ta shiga yajin aiki a Ranar Litinin kan karin alawus

COVID-19: Kungiyar NARD za ta shiga yajin aiki a Ranar Litinin kan karin alawus

Kungiyar NARD ta likitocin da ke neman kwarewa a aiki ta ce yajin da ta daka zai soma aiki ne a yau Litinin, 7 ga watan Satumba, 2020.

Likitocin asibitocin kasar za su tafi yajin aiki a sakamakon gaza zama da shugabanninsu da gwamnatin tarayya ta yi a ‘yan kwanakin bayan nan.

Bayan tafiya yajin aiki, kungiyar NARD ta yi kira ga sauran kungiyoyin ma’aikatan asibiti ta mara mata baya a wannan gwagwarmaya da ta ke yi.

Kungiyar NARD ta bukaci ungonzoma da masu bada magani da sauran likitoci su amsa wannan kira domin ganin an kara yawan alawus din da ake ba su

Jaridar Punch ta fitar da rahoto cewa kungiyar NARD ta na fafatukar ganin an karawa Malamai alawus ne a sakamakon hadarin da su ke fuskanta a bakin aiki.

A Najeriya, N5, 000 kacal ne alawus din da gwamnati ta warewa likitoci saboda yiwuwar fuskantar hadari.

KU KARANTA: Manyan ‘Yan kasuwa sun yabawa Shugaba Buhari kan janye tallafi

COVID-19: Kungiyar NARD za ta shiga yajin aiki a Ranar Litinin kan karin alawus
Kungiyar Likitoci ta na kukan karancin alawus
Source: Depositphotos

Zuwa ranar Lahadi, sakataren yada labarai na NARD, Dr. Stanley Egbogu, ya tabbatarwa ‘yan jarida cewa gwamnati ba ta kira su domin su zauna ba.

Dr Stanley Egbogu ya ke cewa: “Gwamnatin tarayya ba ta gayyacemu domin a zauna ba bayan mun sanar da ita cewa za mu garzaya yajin aiki.”

“Mun fadawa ‘ya ‘yanmu da ke fadin asibotocin jihohi da na gwamnatin tarayya su shiga yajin aikin da mu ka dakatar a ranar 22 ga watan Yuni, 2020.”

“Mu na kira ga sauran kungiyoyin malaman lafiya, NMA, PSN, NANNM, su mara mana baya, su goyi bayan kiran da mu ke yi na kara mana alawus din hadari daga N5, 000.”

NARD ta ce: “Maganar gaskiya ita ce hadarin da mu ke shiga ciki a yau saboda annobar COVID-19, da cututtukan Hepatitis B da C ya zarce abin da mu ka saba fuskanta.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel