An Kama Sojan Najeriya Ya Yi Lalata da Matar Abokin Aikinsa, An Yanke Masa Hukunci
- Wata kotun soja ta musamman ta yanke wa wani Laftanal hukuncin shekaru uku a gidan yari tare da korarsa daga aikin sojan ruwa
- An samu Laftanal din da laifin yin lalata da matar wani jami’in soja da kuma aikata ayyukan da suka sabawa dokar aiki
- An rahoto cewa hukuncin ya fara aiki tun daga ranar 23 ga Nuwamba, 2024, kuma an aiwatar da shi a dandalin horo na NNIT, Sapele
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Rundunar sojan ruwa ta Najeriya (NN) ta kori wani jami’i mai mukamin Laftanal daga aiki tare da yanke masa hukuncin shekaru uku a gidan yari.
Rahoto ya bayyana cewa an yanke wa sojan wannan hukuncin ne bayan da aka same shi da laifin kulla alaƙar soyayya da matar wani soja, har ta kai su ga lalata.

Source: UGC
An samu soja da laifuffuka 4
Kotun soja ta musamman (SCM) ce ta yanke hukuncin, bayan gudanar da shari’ar sojan bisa umarnin hedikwatar rundunar a Abuja, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun tabbatar da cewa an gurfanar da jami’in bisa zargin aikata laifuffuka guda hudu, ciki har da yin lalata da matar soja, wanda ya sabawa sashi na 79 na dokar sojoji (AFA) CAP A20 LFN 2004.
Haka kuma, an tuhume shi da aikata abin kunya da bai dace da matsayin soja ba, wanda ya saba wa sashe na 91, da kuma yaudarar shaida har sau biyu, laifin da ya saba wa sashe na 122 na dokar ta'addanci (CCA), bisa ga sashin 114 na AFA.
An ba sojan damar kare kansa gaban kotu
Majiyoyi sun ce kotun sojin ta gudanar da shari’ar cikin adalci tare da ba jami’in damar kare kansa, daga farko har zuwa lokacin kammala shari’ar.
Rahoton Pulse.ng ya nuna cewa an bi dukkan matakan da doka ta tanada kafin a yanke wa sojan hukuncin.
Daga karshe, an rahoto cewa rundunar sojan ruwa ta amince da hukuncin korar jami'in daga aiki tare da yanke masa hukuncin shekaru uku a gidan yari.

Source: Twitter
Hukuncin ya yi daidai da dokar soja
Rundunar sojan ruwa ta bayyana cewa hukuncin ya yi daidai da sashi na 117(7) na dokar AFA, wanda ke umartar cewa za a kori jami’in da kotun soja ta yanke masa hukuncin zaman gidan yari.
An rahoto cewa hukuncin ya fara aiki tun daga ranar 23 ga Nuwamba, 2024, kuma an fara hukunta sojan a dandalin horo na cibiyar fasahar sojin ruwan Najeriya (NNIT), da ke Sapele, a ranar 29 ga Agusta, 2025.
A cewar majiyar tsaro, wannan hukunci na daga cikin matakan da rundunar ke ɗauka don tabbatar da ladabi, gaskiya da kuma kiyaye mutuncin sojoji yayin da suke aiki.
Soja ta ce manyan jami'ai na cin zarafinta
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata soja ta fito ta zargi manyan jami'an sojojin Najeriya da azabtar da ita sabuwa ta ki yarda su yi lalata da ita.
A cikin wani bidiyo da ta dauka, sojar ta ce an kore ta daga gidanta, an kuma kai ta asibitin masu tabin hankali duk don a ci zarafinta.
Ba iya nan ta tsaya ba, sojar ta ce kin amincewa da bukatar shugabanninta na yin lalata da ya sa an daskarar da asusun bankinta, kuma ta samu tasgaro a aiki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


