MURIC Ta Kausasa Harshe kan Kisan Matar da ake Zargi da Kalaman Batanci a Neja

MURIC Ta Kausasa Harshe kan Kisan Matar da ake Zargi da Kalaman Batanci a Neja

  • Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta yi Allah-wadai da kashe wata mata a Neja da wasu fusatattun matasa suka yi
  • An zargi matar mai suna Amaye da yin maganar batanci ga Annabi Muhammad (SAW) a inda ta ke kasuwancinta
  • MURIC ta bukaci rundunar ‘yan sanda ta Neja ta gaggauta gurfanar da wadanda ake zargi da kalaman a gaban kotu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Niger – Kungiyar kare hakkin Musulmi ta Najeriya (MURIC) ta yi Allah-wadai da kisan wata mata da aka bayyana da suna Amaye.

Rahotanni sun bayyana cewa matasa sun aukawa wa matar bisa zargin kalaman batanci a Kasuwan-Garba, karamar hukumar Mariga, jihar Neja.

MURIC ta magantu kan kisan mata a Neja
Hoton babban Sufeton 'yan sanda, Kayode Egbetokun Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa a cikin wata sanarwa da shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ya sanya wa hannu a ranar Litinin, MURIC ta ce matasan ba su bi tsarin addini ba.

Kara karanta wannan

NDLEA ta kama tsoho mai shekara 70 da miyagun kwayoyi, an lalata gonar wiwi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

MURIC ta magantu kan kisan mata Neja

PM News ta wallafa cewa a cewar MURIC, ta ce harin da aka kai wa matar ba bisa ka’ida ba ne, kuma ba na Musulunci ba, tare da kira ga ‘yan sanda da su dauki matakin gaggawa.

Rahoton ya bayyana cewa Amaye, wacce ke sayar da abinci, ta samu sabani da wani abokin ciniki, inda ake zargin ta yi maganar batanci game da Annabi Muhammad (SAW).

Wannan lamarin ya auku ne da yammacin Asabar, 30 ga watan Agusta, 2025, inda rahotanni suka ce taron jama’a ya mamaye jami’an tsaro kafin daga bisani su banka wa matar wuta.

Taswirar jihar Neja
Tawirar jihar Neja Hoto: Legit.ng
Source: Original

Farfesa Akintola ya ce:

“MURIC ta yi Allah-wadai da wannan kisa."

Kiran kungiyar MURIC ga 'yan sanda

Shugaban MURIC ya bayyana cewa dole ne a gurfanar da wadanda suka aikata kisan a gaban kotu domin daukar matakin da ya dace.

Ya kuma bukaci rundunar ‘yan sandan jihar Neja da ta gaggauta kamawa, tsarewa da gurfanar da su a gaban kuliya.

Kara karanta wannan

Ribadu ya karyata El-Rufai, ya zarge shi da siyasantar da matsalar tsaro

Kungiyar mai kare hakkin Musulmi ta yi kira ga ‘yan sanda da su yi gaggawa wajen tabbatar da cewa duk wadanda suka yi hannun riga a wannan aika-aika sun fuskanci hukunci.

Kungiyar ta ce domin hakan zai zama izina ga sauran jama’a wajen guje wa irin wannan tashin hankali a nan gaba.

Matasa sun hallaka wata mata a Neja

A wani labarin, kun ji yadda Mutane sun gamu da tashin hankali a jihar Neja bayan wasu matasa da suka fusata suka kashe wata mata mai sayar da abinci da aka fi sani da Ammaye.

Wannan mummunan lamari ya auku ne a karamar hukumar Mariga, inda matasan suka zarge ta da fadin kalaman batanci ga Shugaban halitta, Annabi Muhammad (SAW).

Lamarin ya faru ne a Kasuwan Garba, inda shaidu suka bayyana cewa cece-kuce ya fara tsakaninta da wani saurayi da ya bayyana mata cewa yana so ya aureta don raya sunnah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng