Ribadu Ya Karyata El-Rufai, Ya Zarge Shi da Siyasantar da Matsalar Tsaro
- Ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa ya karyata ikirarin Nasir El-Rufai kan ba ‘yan bindiga kudi
- Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta taba shiga yarjejeniyar fansa ko bayar da alawus ga ‘yan ta’adda ba
- ONSA ya ce kalaman Nasir El-Rufai rashin adalci ne ga sojojin da suka rasa rayukansu a yaki da ta’addanci a Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa (ONSA) ya karyata ikirarin Nasir El-Rufai na cewa gwamnatin tarayya na biyan kudin fansa da alawus ga ‘yan bindiga.
ONSA ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Zakari Mijinyawa ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce zargin El-Rufai ba shi da tushe, domin ya saba da gaskiyar abubuwan da ke faruwa a kasa.

Kara karanta wannan
Ba boye boye: El Rufa'i ya magantu kan zargin muzgunawa Kiristocin Kudancin Kaduna

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanan ne a cikin wani sako da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta kuma jaddada cewa gwamnatin tarayya tun farko ta yi gargadi ga ‘yan Najeriya da su guji biyan kudin fansa, domin hakan na karfafa wa masu aikata laifi gwiwa.
Zargin da El-Rufai ya yi wa gwamnati
A ranar Lahadi, El-Rufai ya bayyana a Channels Television inda ya zargi gwamnatin tarayya da daukar hanyar sulhu da ‘yan bindiga.
Ya ce:
“Gwamnati ta rungumi manufar yin sulhu da ‘yan bindiga da kuma basu alawus, maimakon tunkararsu da karfin soja. Wannan manufar karfafa su ne kawai.”
Tsohon gwamnan ya bayyana wannan salon a matsayin dabarar da ke bai wa ‘yan bindiga damar samun karfi a maimakon a rage musu.
'El-Rufa'i bai girmama sojoji ba,' ONSA
Sanarwar ONSA ta bayyana cewa kalaman El-Rufai rashin adalci ne ga dubban jami’an tsaro da suka sadaukar da rayukansu wajen yaki da ta’addanci.
Punch ta wallafa cewa sanarwar ta ce:
“Babu wani lokaci da ONSA ko wata hukuma a karkashin wannan gwamnati ta taba shiga yarjejeniya ta biyan kudin fansa ga ‘yan ta’adda.
Akasin haka, mun rika gargadin jama’a da su guji biyan kudin fansa.”

Source: Twitter
Nasarorin yaki da ‘yan bindigan Najeriya
Sanarwar ta ce tsarin ya samar da sauki a wasu yankuna da suka sha fama da hare-hare a Kaduna, ciki har da Igabi, Birnin Gwari da Giwa, inda yanzu ake samun zaman lafiya fiye da baya.
Haka kuma, Malam Nuhu Ribadu ya yi addu’ar rahama ga jami’an tsaro da suka rasa rayukansu a kokarin tabbatar da tsaron kasa.
Ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro ya ce bai kamata a raina sadaukarwar wadannan jarumai ta hanyar yin ikirarin da ba shi da tushe.
El-Rufa'i ya musanya zargin ware Kudancin Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa Malam Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa bai ware yankin Kudancin Kaduna ba a lokacinsa.

Kara karanta wannan
'Ba don addini ba ne,' El Rufa'i ya fadi dalilin kawo tikitin Muslim Muslim a 2023
Ya bayyana cewa akwai matakan da ya dauka domin daidaita lamura a jihar ba wai domin nuna wariya ba.
Baya ga haka, El-Rufa'i ya ce bai damu da makiyansa da ke sukar shi ba, saboda rayuwarsa ba ta gudana a karkashin abin da suke fada.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
