Sokoto: Gwamna Zai Fara ba Limamai, Ladanai da Masallatan Juma'a Kudin Wata
- Gwamnatin Sokoto za ta rika biyan alawus ga limamai, na’ibansu da ladanai tare da tallafa wa masallatan Juma’a a duk fadin jihar
- Gwamna Ahmed Aliyu ya ce tallafin kudi daga N300,000 zuwa N500,000 da alawus na wata-wata zai karfafa koyar da addinin Musulunci
- Sarkin Musulmi da sauran shugabanni sun yaba da matakin gwamnati tare da karfafa yara wajen haddar Alkur’ani da zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Sokoto - Gwamnatin Sokoto ta bayyana cewa za ta fara biyan alawus din kudi ga limamai, na’ibansu da ladanai a dukkan masallatai.
Haka kuma, Gwamnatin Ahmad Aliyu za ta fara ware kaso mai tsoka na tallafi ga masallatan Juma’a na Izala da Darika da ke a fadin jihar.

Source: Facebook
Sokoto: Za a rika ba limamai kudin wata
Mai magana da yawun gidan gwamnati, Abubakar Bawa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Asabar, inji jaridar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubakar Bawa ya ce wannan mataki na cikin shirye-shiryen gwamnatin Ahmed Aliyu na karfafa yada addinin Musulunci da taimakawa yara wajen haddar Alkur’ani.
Sanarwar ta ce Gwamna Ahmad Aliyu ya sanar da tallafin ne a yayin bikin saukar Alkur’ani na dalibai 111 da gidauniyar Sheikh Dahiru Usman Bauchi, reshen Sokoto ta shirya.
Ya ce alawus din zai taimaka wa malamai wajen sauke nauyin da ke kansu yadda ya kamata tare da tabbatar da ci gaban koyarwar Musulunci.
Gwamna Ahmad Aliyu ya ce:
“Mun samar da rabon kudi ga masallatan Juma’a daga N300,000 zuwa N500,000 bisa matsayinsu. Haka kuma mun kafa alawus na wata-wata ga limamai, na’ibansu da ladanai domin tallafa musu wajen gudanar da ayyukansu."
An karfafa yara kan karatun Alkur'ani
Gwamnan ya ce harkokin addini na daga sahun gaba a gwamnatin sa a karkashin shirin Nine-Point Smart Agenda, inda yake matsayin na biyu bayan tsaro.
Ya kara da cewa ƙarfafa yara kan haddar Alkur’ani zai samar da al’ummar da ke bin sunnonin Annabi Muhammad (SAW).
A taron, Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar ya yi jinjina ga Sheikh Dahiru Bauchi bisa kafa wannan gidauniya, tare da yabawa malamai a jihar saboda kokarinsu na yada akidun Musulunci da tabbatar da zaman lafiya.
Tsohon gwamnan Sokoto, Aliyu Wamakko wanda Aminu Sufi ya wakilta, ya shawarci iyaye da su karfafa wa ’ya’yansu gwiwa wajen haddar Alkur’ani.

Source: Facebook
An ba masu saukar Al'kur'ani kyaututtuka
A nasa bangaren, Sanata Abdulaziz Yari wanda Lawal Liman ya wakilta, ya ba da tallafin Naira miliyan 22 da kayan abinci ga makarantar da daliban da suka yi sauka.
Shi kuwa Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi, wanda Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya wakilta, ya ce an fadada makarantar zuwa wasu jihohi domin ba yara dama su ci gaba da karatu cikin tsari, tare da rage barace-barace a tituna.
Dukkan daliban 111 da suka yi saukar sun samu kyautar N20,000 da tufafi daga gwamnatin jihar Sokoto, inda bikin ya gudana da karatun Alkur’ani da kuma rabon kyaututtuka.

Kara karanta wannan
Ana hallaka jama'ansa, Gwamna Radda zai kashe Naira miliyan 680 a gyaran maƙabartu
Gwamna Radda ya sa wa limami alawus
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan Katsina ya ce yaki da rashin tsaro shi ne babban ajandar gwamnatinsa tun daga ranar farko da ya hau karagar mulki.
Da wannan, Gwamna Dikko Radda ya amince da karin albashi ga dagatai da tallafin kudi ga masu unguwanni 6,652, limamai sama da 3,000 da masu share masallatai.
Gwamnatin Dikko Radda ta kuma ware Naira miliyan 20 ga kowace karamar hukuma domin gyaran makabartu a fadin jihar Katsina.
Asali: Legit.ng

