'Gado Na Yi': Malamin Addini da Ake Zargi da Aukawa Ƴarsa Tsawon Shekaru 4 Ya Magantu
- Mutane sun shiga wani irin yanayi bayan cafke malamin addinin da ke cin zarafin yarsa har na tsawon lokaci
- Faston mai shekaru 42, Samson Ajayi, ya shiga hannun hukuma bayan ya amsa laifin aukuwa ‘yarsa na tsawon shekaru hudu
- A cewar lauyan gwamnati, laifin ya faru a kai-a kai daga 2021 zuwa 2025 a Igoba, kuma ya sabawa dokokin hana cin zarafi na Ondo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Akure, Ondo - Wani Fasto mai shekaru 42 ya shiga hannu kan zarge-zarge da suka hada da cin zarafin ƴarsa da aka ce ya shafe tsawon shekaru hudu yana yi.
An umarci tsare wanda ake zargin mai suna Samson Ajayi a gidan gyaran hali bayan tuhume-tuhumen cin zarafin ‘yarsa.

Source: Original
'Gado na yi': Fasto bayan zargin cin zarafi
Rahoton Vanguard ya ce Ajayi ya amsa laifin, inda ya shaida wa kotu cewa “tsafi ne da ya gada a gida” ya rinjaye shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ajayi ya tabbatar da cewa mahaifinsa ma ya taba cin zarafin ‘yar’uwarsa shekaru da dama da suka wuce.
Lauyan gwamnati, Martins Olowofeso, ya bayyana wa kotu cewa cin zarafin ya rika faruwa a kai-a kai tun daga watan Maris 2021 har zuwa Agusta 2025 a gidansu da ke Igoba.
Ya ce wannan laifi ya sabawa dokar hana cin zarafin mutane ta jihar Ondo da aka kafa a shekarar 2021.
A cikin takardar tuhuma, an bayyana cewa:
“Kai Samson Ajayi, tsakanin watan Yuli 2021 da Agusta 2025 a Igoba, ka yi lalata da ‘yarka mai shekaru 17.”

Source: Twitter
An tura Fasto gidan gyaran hali a Ondo
Lauyan gwamnati ya bukaci kotu ta tsare shi a gidan gyaran hali, yayin da ake jiran shawarar ofishin Lauyan Gaba (DPP).
Ajayi ya yi bayani cewa:
“Ban san abin da ya same ni ba, ina ganin tsafi na gado ne, domin mahaifina ma ya taba yi wa ‘yar’uwarsa haka.”
Lauyansa, Kehinde Osadugba, ya roki kotu ta ba shi damar sulhu, saboda uwargidansa ta yafe masa ganin shi ne ke ciyar da gida.
An kuma saka ranar cigaba da shari'ar
Sai dai Alƙali Taiwo Lebi ya ƙi amincewa da roƙon, ya ce amincewar Ajayi ta tabbatar da dalilin tsarewa.
Ya umarci a mika fayil ɗin karar zuwa ga DPP domin ƙarin shawarwari game da zargin da ake yi masa.
An dage sauraron shari’ar har zuwa ranar 20 ga watan Nuwambar shekarar 2024 da muke ciki domin ci gaba da tattaunawa kan batun karar.
An kama limami kan zargin cin zarafi
A baya, mun kawo muku cewa rundunar ‘yan sandan Osun ta kama wani malamin addini da ake zargi da lalata wata yarinya ‘yar shekara takwas a Ede.
Lamarin ya faru a unguwar Babasanya-Araka inda jama’a suka taru suka kai hari kan wanda ake zargin kafin a mika shi ga Amotekun.
Kwamandan Amotekun da wasu mazauna sun tabbatar da cewa wanda ake zargin limami ne kuma yana koyar da Alkur’ani a unguwar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

