Wa'iyazubillah: Tsoho dan shekara 60 ya lalata wata karamar yarinya

Wa'iyazubillah: Tsoho dan shekara 60 ya lalata wata karamar yarinya

- Jami'an 'yan sanda a jihar Anambra sun kama wani tsoho dan shekara 60 mai suna, Mista Okafor Ndubuisi

- Ana zargin Ndubuisi da lalata da wata karamar yarinya mai shekara 9 a duniya

- An tattaro cewa tsohon ya lalata yarinyar sau da dama a cikin dakinsa

- Kakakin yan sandan jihar Anambra, SP Haruna Mohammed, ya tabbatar da faruwar lamarin

Wani tsoho dan shekara 60 mai suna, Mista Okafor Ndubuisi, ya shiga hannun ‘yan sanda kan zargin lalata karamar yarinya ‘yar shekara 9 a karamar hukumar Oyi da ke jihar Anambra.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar wanda ake zargin ya sha lalata da yarinyar sau da dama a dakinsa.

Da yake tabbatar da lamarin, kakakin yan sandan jihar Anambra, SP Haruna Mohammed, ya ce yan sandan da ke aiki a sashin 3-3, Nkwelle Ezunaka a karamar hukumar Oyi, sun kama Okafor Ndubuisi kan zargin lalata yarinya yar shekara 9.

Wa'iyazubillah: Tsoho dan shekara 60 ya lalata wata karamar yarinya
Wa'iyazubillah: Tsoho dan shekara 60 ya lalata wata karamar yarinya Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

Ya bayyana a wani jawabi cewa: “a ranar 12 ga watan Yulin 2020, da misalign karfe 2:30 na rana biyo bayan wani korafi da duka samu, jami’an ‘yan sandan sashi na 3-3 su kama wani Okafor Ndubuisi, mai shekara 60 a Sun Rise Estates Nkwelle Ezunaka a karamar hukumar Oyi na ihar Anambra.

“Wanda ake zargin, a wannan rana kuma a lokuta mabanbanta, ya yi lalata da yarinya ‘yar shekara 9 a dakinsa.

KU KARANTA KUMA: Kwamitin shugaban kasa: Magu ya mayar da EFCC kamar wani babban ofishin 'yan sanda

“’Yan sanda sun ziyarci wajen sannan suka dauki yarinyar zuwa asibiti domin a duba ta.”

Ya ce kwamishinan yan sanda, CP John Abang, ya yi umurnin mayar da lamarin zuwa ga sashin binciken laifuka, Awka domin bincike da kyau inda daga nan za’a mika wanda ake zargin zuwa kotu.

A gefe fuda, an gurfanar da wani dan shekaru 32, Mohammed Zulfaralu, a gaban wata babbar kotun majiatare da ke zama a Kano kan zargin yi wa tsohuwa yar shekaru 85 fyade.

An gurfanar da matashin ne a ranar Laraba, 1 ga watan Yuli.

Wanda ake karan, Zulfaralu, wanda ke zaune a Gidan Kwana, kauyen Kwanar Dangora, yana kuma fuskantar tuhuma na yunkurin yi wa matan aure uku fyade.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel