Uba Sani Ya Maido Malaman da El Rufa'i Ya Kora daga Bakin Aiki a Kaduna

Uba Sani Ya Maido Malaman da El Rufa'i Ya Kora daga Bakin Aiki a Kaduna

  • Gwamnatin Uba Sani a Kaduna ta jawo wa kanta yabo daga kungiyar kwadago ta kasa (NLC) kan waiwayar malaman jihar da aka kora
  • A lokacin tsohuwar gwamnatin jihar a karkashin Malam Nasir El Rufa'i ne aka kori malamai akalla 23,000 bisa zargin rashin cancanta
  • Shugaban NLC na jihar, Ayuba Suleiman, ya bayyana cewa an fara maido da shugabannin makarantu da wasu daga cikin malaman da aka kora

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna – Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) reshen Kaduna ta jinjinawa Gwamna Uba Sani bisa matakin dawo da wasu daga cikin malaman da gwamnatin baya ta kora a jihar.

Shugaban NLC na jihar, Ayuba Suleiman, ne ya bayyana haka a yayin da yake ganawa da 'yan kungiyar 'yan jarida masu binciken bin diddigi (NGIJ) waɗanda ke jihar.

Kara karanta wannan

Yadda uwargidan Gwamnan Borno ta gwangwaje mai shara da kyaututtuka bayan mayar da N4.8m

Gwamnan Kaduna ya fara maido malaman makaranta bakin aiki
Uba Sani (H), Nasir El-Rufa’i Hoto: Senator Uba Sani/Nasir El-Rufa’i
Source: Facebook

Daily Nigerian ta ruwaito cewa a shekara ta 2018 zuwa 2021, tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya sallami fiye da malamai 23,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin ma'aikatan da aka sallamar har da tsohon shugaban kungiyar malaman makaranta na kasa, NUT.

Gwamnatin Uba Sani ta waiwayi korarrun malamai

NAN ta wallafa cewa Ayuba Suleiman ya ce gwamnatin Uba Sani ta riga ta dawo da shugabannin makarantun da aka kora bakin aiki.

Haka kuma ta dawo da malaman kimiyya da wasu rukuni na malaman, inda gwamnati ta ce wannan mataki na gyara kura-kuran da suka faru a baya.

Game da batun sabon mafi ƙarancin albashi, shugaban kungiyar ya bayyana cewa gwamnan ya amince da biyan ₦72,000 ga ma’aikata daga mataki na 1 zuwa 7, kuma an riga an fara aiwatar da shi.

Ya ce:

"Mun godewa gwamna bisa wannan mataki da ya dauka a kan mafi karancin albashi. Yanzu haka ana tattauna yadda za a yi wa manyan ma'aikata karin da ya dace."

Kara karanta wannan

Gwamna ya samu gagarumin goyon baya, ana so ya nemi takarar shugaban kasa a 2027

"Gwamnati za ta bukaci akalla N1.2bn domin ta tabbatar da sabon tsari ga ma'aikatan jihar."

NLC ta yabi gwamnatin jihar Kaduna

Baya ga haka, Ayuba Suleiman ya yaba da matakin gwamnati na fitar da bas 20 domin jigilar ma’aikata da ɗalibai kyauta a matsayin taimako kan tsadar rayuwa da ta biyo bayan cire tallafin man fetur.

A wani bangare na ziyararsu, 'yan jarida na kungiyar NGIJ sun ce suna gudanar da tambayoyi tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki a kananan hukumomi 23 na jihar Kaduna.

NLC ta yaba wa gwamnan Kaduna
Hoton gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

Sun ce ana haka ne domin nazari kan yadda ake tafiyar da mulki a jihar, kuma za su tattara bayanansu ddomin fitar da rahoto a kan hakan.

Gwamnatin Kaduna ta kori malamai

A baya, mun wallafa cewa Hukumar Ilimi Bai Daya ta Jihar Kaduna (KADSUBEB) ta sanar da cewa ta kori malamai 2,357 daga aiki bayan faduwa a jarabawar cancanta da aka gudanar.

Mai magana da yawun hukumar, Mrs. Hauwa Mohammed ta ce watan Disambar 2021 hukumar ta gudanar da jarabawar cancanta ga malamai fiye da 300,000.

A cewar sanarwar, daga cikin malamai da aka sallama akwai malamai 2,192 na makarantu na firamare, ciki har da shugaban kungiyar malaman makarantu na kasa (NUT), Mr. Audu Amba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng