Santaleleliyar Budurwa Ta Rasa Ranta yayin Zubar Ciki, an Gano Abin da Ya Faru
- Mutane da dama sun shiga wani irin yanayi bayan mutuwar wata ɗaliba da ke shekarar karshe a Kwalejin Fasaha
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa dalibar ta rasa ranta ne yayin da take kokarin zubar da cikin da alama ba ta san ta haifa
- Dalibar ‘yar ajin karshe a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kogi ta mutu a asibiti lokacin da ake kokarin raba ta da cikin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lokoja, Kogi - Rundunar yan sanda a jihar Kogi ta ziyarci wani asibiti da wata santaleleliyar budurwa ta mutu.
An tabbatar da cewa marigayiyar daliba ce da ke shekarar karshe a Kwalejin Fasaha da ke jihar.

Source: Original
Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa dalibar ta rasa ranta ne a kokarin zubar da ciki.
Me doka ta ce kan zubar da ciki?
A Najeriya akwai dokoki da aka tanadar kan zubar da ciki da mata ke yi wanda idan aka samu mutum da laifi zai dandana kudarsa.
Binciken Centre for Reproductive Rights ya bayyana hukunci kan masu zubar da ciki da gangan saboda wata manufa ta su musamman a Arewacin Najeriya.
Rahoton ya ce idan wani ya yi sanadin zubar da cikin mace da gangan ba wai domin ceto rayuwarta ba zai fuskanci dauri a gidan kaso.
Rahoton ya ce:
"Duk wanda da gangan ya sa mace mai juna biyu ta zubar da ciki, idan ba a yi hakan domin ceton rayuwarta ba, za a hukunta shi da ɗaurin shekaru har zuwa 14, ko tara, ko kuma duka biyun."

Source: Twitter
Budurwa ta mutu yayin zubar da ciki
An ce dalibar ta mutu yayin da ake yi mata aikin zubar da ciki a wani asibitin da ke birnin Lokoja.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 26 ga watan Agustan 2025 a Asibitin Al-Hassan Clinic and Maternity, Sarkin Noma, Lokoja.
An gano cewa marigayiyar, mai suna Omotosho Dorcas, mai shekaru 26, na dauke da ciki na wata shida lokacin da ta je neman zubar da cikin.
"Yayin da ake kokarin zubar da cikin, ta fara zubar da jini wanda ya yi sanadin mutuwarta nan take."
- Cewar wasu majiyoyi
Har ila yau, ‘yan sanda sun kai ziyara wurin, sun dauki hotuna sannan suka dauki gawarta zuwa asibitin gwamnatin tarayya da ke Lokoja.
Sun kuma ce an cafke wanda ake zargi da kokarin zubar da cikin, za a mika batun ga jami'an SCID domin ci gaba da bincike.
Yadda likitan bogi ke zubar da cikin mata
A baya, kun ji cewa wani bincike ya nuna yadda wani “likitan boge” mai suna Ali Madida ya ke zubar wa 'yan mata ciki a unguwar Yan-Doya da ke Jos a jihar Plateau.
An kuma zargi Madida, da kashe wata budurwa, Halima, a wajen zubar mata da ciki da kuma jefa 'yan mata a harkar karuwanci a yankin.
Yayin wani binciken sirri, an tattara rahoton tare da tallafi daga Cibiyar Rediyon Mata da Gidauniyar MacArthur da ke ba da tallafi a harkar jarida da bincike.
Asali: Legit.ng

