Kudin Fansa: 'Yan Bindiga Sun Dauke Mutum 4700, An ji Biliyoyin da Aka Rasa a Shekara 1
- Najeriya na ci gaba da fama da rashin tsaro musamman a Arewacin kasat daga garkuwa da mutane da ta'adin 'yan Boko Haram
- Wani rahoton bincike ya bayyana cewa, a cikin shekara guda, ‘yan Najeriya sun biya biliyoyin kudi a matsayin kudin fansa ga masu garkuwa
- Rahoton ya gargadi gwamnati ta dauki matakan gaggawa da lalata hanyar kudaden shiga na masu garkuwa, domin hana wannan sana’a ta zama babba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Hukumar binciken siyasa da tsaro, 'SB Morgen (SBM) Intelligence', ta fitar da rahoto kan yawan biliyoyi da yan bindiga ke karba.
Rahoton ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane sun bukaci sama da N48bn daga hannun jama'a tsakanin Yuli 2024 zuwa Yuni 2025.

Source: Facebook
Rahoto ya bankado munin ta'addanci a Najeriya
Hakan na cikin sabon rahotonsu da suka kira “Economics of Nigeria’s Kidnap Industry” wanda jaridar TheCabe ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton ya bayyana cewa daga cikin wannan adadi na biliyoyi da aka nema, an biya N2.57bn ne kacal ba kari.
SBM ta ce akalla mutane 4,722 aka sace a hare-hare 997, inda mutane 762 suka mutu a wannan lokaci.
SBM ta bayyana cewa yankin Arewa maso Yamma ne mafi muni, yayin da Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu ke fuskantar satar saboda addini da neman kudi.
Yawan kudin fansa da aka biya a 2022
Misali, a rahoton 2022 an biya N653.7m wanda ya yi daidai da $1.13m, sai ya sauka zuwa N302m a 2023, Vanguard ta tabbatar.
Rahoton ya ce wannan bambancin ya nuna yadda ake samun koma-baya a darajar Naira, wanda ya kara sa garkuwa da mutane zama babbar sana’a.
SBM ta bayyana cewa masu laifin suna kara bukatar Naira mai yawa domin su daidaita da raguwar karfin sayen kudin kasar.
Rahoton ya kara da cewa hakan ya sauya garkuwa daga matsalar tsaro kawai zuwa wata sana’a da ke ci gaba da bunkasa.

Source: Facebook
Jihohin da suka fi fama da ta'addanci
A nazarin jihohi, an gano cewa Zamfara, Kaduna da jihar Katsina sun fi yawan wadanda aka yi garkuwa da su a cikin wannan shekara.
"A lokutan da aka yi wannan bincike, Katsina ce kan gaba da yawan kai hari har sau 131 da ya kai kashi 13 a Najeriya baki daya.
"Sai dai hakan ya gaza da yawan mutane da aka sace a Zamfara ba wanda ya kai jama'a 1203, hakan ya kai kashi 24 kenan."
SBM ta ce daga cikin jihohi biyar da ke gaba a yawan hare-hare, hudu daga Arewa ne, ciki har da Katsina, Kaduna, Zamfara da Niger.
Delta ce kadai daga Kudu ke cikin jerin, inda aka samu hare-hare 49, wanda bai kai kashi 5% na gaba ɗaya ba.
An fadi yawan kungiyoyin ta'addanci a Afirka
Kun ji cewa tsohon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya ce sama da kungiyoyin ta’addanci 1,000 ke aiki a Afrika.
Ya yi kira ga shugabannin Nahiyar da su gina masana’antar tsaro don fuskantar barazanar da ke damun yankinsu.
Farfesa Gambari ya fadi haka ne a wani taron tsaron Afrika da aka gudanar Abuja tare da halartar kasashe 36 daga cikin 54 na Nahiyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


