'Yan Sanda Sun Dauki Mataki yayin da Masu Mauludi Suka Fara Zagayen Gari a Jigawa
- Kungiyar Zawiyya Islamiyya da rundunar 'yan sanda sun yi zama na musamman a Jigawa, yayin da aka shiga watan Mauludi
- Tare da Zawiyya, akwai kuma kungiyar kabilun da ba 'yan asalin Jigawa ba, inda aka tattauna kan bukukuwan Maulidi a jihar
- Rundunar 'yan sandan Jigawa, karkashin CP Dahiru Muhammad ta fada wa kungiyoyin matakan da aka dauka kan Mauludi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jigawa - Rundunar ‘yan sanda a Jigawa ta tabbatar da cewa an ɗauki tsauraran matakan tsaro domin gudanar da bukukuwan Mauludi cikin kwanciyar hankali a fadin jihar.
Rabi’ul Awwal shi ne wata na uku a kalandar Musulunci, kuma Musulmai a duniya ke girmamawa saboda shi ne watan da aka haifi Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi).

Source: Twitter
An shiga watan bikin Mauludi
Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, wanda shi ne shugaban majalisar koli ta harkokin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ya sanar da cewa Litinin, 25 ga Agusta 2025, ita ce ranar farko ta Rabi’ul Awwal 1447 AH, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana gudanar da bikin Mauludi, wanda ake kira Mawlid an-Nabi, ta hanyar yin addu’o’i, karatun Alkur’ani, hudubobi, tarukan jama’a da kuma ayyukan alheri a duk tsawon watan.
A Najeriya, ciki har da Jigawa, ana gudanar da Mauludi ta hanyar ibada, zagayen gari, tarukan majalisi, tarukan sha'irai da sauran bukukuwa, inda al’umma ke taruwa don girmama koyarwar Annabi tare da jaddada zumunci da haɗin kai.
Zawiyya ta ziyarci 'yan sanda kan Mauludi
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda, SP Shi’isu Adam, ya bayyana cewa rundunar ta dauki tsauraran matakai don tabbatar da tsaro yayin bikin Mauludi.
SP Adam ya bayyana hakan a Dutse ranar Talata, bayan ziyarar hadin gwiwa da kungiyar ƙabilun da ba 'yan jihar ba tare da kungiyar Zawiyya Islamiyya ta jihar suka kai hedikwatar ‘yan sanda.
Wannan tawaga ta kasance karkashin jagorancin Ibrahim Yahaya Katsina, mai tallafa wa gwamna kan harkokin ƙabilun da ba 'yan jihar ba, da Musa Saminu, sakataren kungiyar Zawiyya Islamiyya.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Dahiru Muhammad, ya tarbi tawagar a ofishinsa, inda ya gode musu bisa goyon baya da haɗin kai da suke bayarwa a kowane lokaci.

Source: Original
Matakin 'yan sanda kan bikin Mauludi
CP Dahiru ya jaddada kudirin rundunar wajen gudanar da aikin tsaro bisa adalci, kwarewa da kuma hada kai da kowace kungiya a jihar.
Kwamishinan ya tabbatar da cewa an kammala shirye-shiryen tsaro don ganin cewa bikin Mauludin bana ya gudana ba tare da wata tangarda ba.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su gudanar da bukukuwan cikin lumana tare da gaggauta sanar da hukumomi idan sun ga duk wata alama ta barazana.
SP Adam ya ce wannan ziyara ta kara tabbatar da haɗin kai tsakanin kungiyoyin al’umma da jami’an tsaro wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar, musamman a manyan bukukuwan addini.
'Yan Tijjaniyya za su yi Mauludi a Yobe
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Gwamna Mai Mala Buni, ya bukaci ‘yan Najeriya su dage da yi wa shugabanni addu’a domin samun jagoranci na gari da zaman lafiya.
Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya bayyana haka ne yayin ganawa da shugabannin Darikar Tijjaniyya karkashin Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi.
Shugaban gidauniyar Sheikh Dahiru Usaman Bauchi, Sheikh Ibrahim Dahiru Bauchi, ya ce sun zo jihar Yobe ne domin bikin mauludin Sheikh Ahmadu Tijjani.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


