Abubuwa 5 da Suka Jawo Rashin Fahimta tsakanin Najeriya da Amurka
Tun farkon shekarar 2025 alakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Amurka ta fara tsami saboda wasu abubuwa.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A baya bayan nan, an samu sabanin kan lamuran diflomasiyya tsakanin gwamnatin tarayyar Najeriya da Amurka.
Sabanin da aka samu game da musayar fursunoni, dokar biza tsakanin kasashen na cikin abubuwan da suka dauki hankalin al'umma da dama.

Source: Getty Images
A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku abubuwan da suka yi kokarin jawo rashin fahimtar juna tsakanin Najeriya da Amurka.
1. Sabani kan dokar bizar Amurka
A kwanakin baya ofishin jakadancin Amurka ya ce dole masu neman biza su lissafa dukkan kafafen sada zumunta da su ke amfani da su yayin neman izinin shiga kasarsa.
Ofishin ya wallafa a X cewa:

Kara karanta wannan
Abin kunya: Amurka ta daure Sarkin Najeriya da ya sace Naira biliyan 6.4 na COVID 19
“Dole masu neman bisa su lissafa dukkan sunayen shafukan sada zumunta da suka yi amfani da su cikin shekaru biyar da suka gabata a takardar neman bisa ta DS-160,”
Ta ƙara da cewa za a bukaci masu neman su tabbatar da cewa bayanan da suka bayar a cikin fom ɗin neman bisa gaskiya ne kafin su sanya hannu da mika shi.

Source: Facebook
Sanarwar ta kara da cewa kin sanya bayanan kafafen sada zumunta na iya haifar da kin amincewa da bukatar neman bizar mutum.
Martanin Najeriya kan dokar bizar Amurka
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Kimiebi Ebienfa, ya ce gwamnati za ta ɗauki irin wannan mataki ga ‘yan Amurka da suke neman bizar Najeriya.
Rahoton DW ya nuna cewa ya ce ma’aikatar Harkokin Waje za ta gudanar da taron haɗin gwiwa da Ma’aikatar Cikin Gida da Hukumar Leken Asiri ta Ƙasa domin tattauna matsalar.
“Za mu yi taro mu amince kan mafi kyawun hanyar da za mu yi martani,”
Inji Ebienfa
2. Najeriya ta ki karbar fursunonin Amurka
A kwanakin baya Najeriya ta ce ba za ta lamunci matsin lambar gwamnatin Donald Trump ba na karɓar ‘yan kasar Venezuela da aka kora ko kuma fursunonin wasu kasashe daga Amurka.
Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Tuggar ne ya bayyana haka a wata hira da aka yi da shi a tashar Channels TV.

Source: Twitter
A cewar shi:
“Mu ma muna da mutane fiye da miliyan 230,”
Ministan wajen ya kara da cewa:
“Ba adalci ba ne a ce Najeriya ta karɓi ‘yan Venezuela 300 da aka kora,”
3. Amura ta laftawa Najeriya haraji
A farkon watan Agusta shugaban Donald Trump ya tabbatar da sanya haraji ga Najeriya da wasu kasashe.
Duk da ƙarin wa’adin da aka bayar domin duba yiwuwar janye harajin, yawancin tattaunawar da aka yi da Amurka ba su haifar da wata sabuwar yarjejeniya ba.
Najeriya tare da wasu kasashen Afrika da dama sun fuskanci karin harajin shigo da kaya har kashi 15 sakamakon wata doka ta musamman da Donald Trump ya rattaba hannu a kanta.

Source: Facebook
4. Amurka ta soki albashin N70,000
Gwamnatin Amurka ta fitar da wani rahoto kan wasu abubuwa da suka shafi Najeriya, musamman bangaren tattali.
Rahoton ya soki kokarin gwamnatin Najeriya na mayar da mafi karancin albashi zuwa N70,000 da gwamnatin Bola Tinubu ta yi.

Source: Facebook
Legit Hausa ta rahoto cewa Amurka ta ce N70,000 ba za ta tabuka komai ba lura da yanayin darajar kudin Najeriya.
5. Amurka ta ki gayyatar Najeriya
A kwanakin baya ne gwamnatin Amurka ta gayyaci wasu shugabannin Amurka taro ba tare da sanya Najeriya a ciki ba.
Legit Hausa ta rahoto cewa, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Aubakar ya ce hakan na cikin abin da ke nuna rashin alaka mai kyau tsakanin kasashen.
Amurka ta yabi Najeriya kan yakar ta'addanci
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta yaba wa Najeriya kan kama shugabannin kungiyar ta'addanci ta Ansaru.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ne ya bayyana nasarar a wani taro a Abuja.
Haka zalika, Birtaniya ta yaba wa Najeriya kan lamarin, inda ta ce kama shugabannin 'yan ta'addan zai taimaka wajen magance matsalar tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

