Duk da Yana Brazil, Shugaba Tinubu Ya Yi Magana kan Hatsarin Jirgin Kasan Kaduna

Duk da Yana Brazil, Shugaba Tinubu Ya Yi Magana kan Hatsarin Jirgin Kasan Kaduna

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya samu labarin hatsarin jirgin kasan da ya ritsa da fasinjoji a kan hanyar Abuja-Kaduna
  • Mai shugaban kasan ya ba da tabbacin cewa duk da ba ya cikin kasar nan a halin yanzu, yana samun rahotanni kan hatsarin jirgin
  • Bola Tinubu wanda ya bar Najeriya tun kwanaki ya bayyana cewa za a dauki matakai don sake hana aukuwar hatsarin a nan gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi magana kan hatsarin jirgin kasan da ya auku a kan hanyar Abuja-Kaduna.

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana bakin cikinsa kan hatsarin da ya faru a layin dogon jirgin kasan Abuja-Kaduna a ranar Talata, 26 ga watan Agustan 2025.

Tinubu ya yi alhini kan hatsarin jirgin kasan Kaduna
Hotunan Shugaba Bola Tinubu da wani bangare na jirgin kasan Abuja-Kaduna da ya yi hatsari Hoto: @OfficialABAT, @SasDantata
Source: Twitter

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a yau Talata, 26 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan

Ta faru ta ƙare: Hukumar jiragen ƙasa ta dakatar da zirga zirga daga Kaduna zuwa Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgin kasan dai ya gamu da hatsarin ne da safiyar ranar Talata lokacin da yake tafiya a kan hanya.

Hatsarin ya auku ne lokacin da jirgin kasan wanda ya taso daga tashar Rigasa ya sauka daga kan layin dogonsa.

Lamarin dai ya sanya wasu daga cikin taragon jirgin wanda yake dauke da fasinjoji sun kife, wanda hakan ya sanya mutane neman hanyoyin tsira.

Me Tinubu ya ce kan hatsarin jirgin kasar?

Mai girma Bola Tinubu ya ce yana bin diddigin lamarin duk da yana ziyarar aiki a kasar Brazil.

Shugaban kasan wanda ya nuna takaicinsa kan lamarin, ya yi addu'a ga wadanda suka samu raunuka sakamakon hatsarin.

"Na shiga matukar damuwa da wannan lamari. Ina mika addu’ata ta musamman ga waɗanda suka ji rauni, iyalansu, da kuma dukkan fasinjojin da suka shiga cikin wannan mummunan hali."

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya kara da cewa yana karɓar rahotanni akai-akai, kuma yana jiran cikakken bayani domin a ɗauki matakan gaggawa.

Kara karanta wannan

NSIB ta gano wasu bayanai kan hatsarin jirgin Kaduna, an ji halin da fasinjoji 6 ke ciki

Shugaban kasan ya bayyana cewa hukumar jiragen kasa ta Najeriya (NRC) na aiki tukuru kan lamarin.

Jirgin kasan Kaduna-Abuja ya yi hatsari
Hoton wasu taragon jirgin kasan Kaduna-Abujada suka kife Hoto: @SasDantata
Source: Twitter

Tinubu ya ce za a dauki mataki kan lamarin

Shugaba Tinubu ya kuma tabbatar da cewa za a ɗauki matakai domin kauce wa maimaituwar irin wannan hatsarin a nan gaba.

"Ina ci gaba da samun sababbin rahotanni, kuma ina jiran cikakken bayani domin a ɗauki matakin gaggawa da tallafa wa duk wadanda abin ya shafa."
"Hukumar NRC ta riga ta shiga cikin lamarin, kuma ana sa ran ɗaukar matakan da suka dace domin hana irin wannan sake faruwa a gaba."

- Shugaba Bola Tinubu

Fasinjoji sun jikkata a hatsarin jirgin Kaduna-Abuja

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar binciken tsaro ta Najeriya (NSIB) ta fitar da bayanai kan hatsarin jirgin kasan da ya auku a kan hanyar Abuja-Kaduna.

A cikin wata sanarwa da hukumar NSIB ta fitar, ta bayyana cewa ba a samu asarar rai ba, amma fasinjoji guda shida sun jikkata.

Ta bayyana cewa ta tura wata tawaga domin tattara shaidu don fara binciken abubuwan da suka jawo aukuwar hatsarin jirgin kasan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng