Makinde: Gwamna Zai Mika Ragamar Mulki ga Mataimakinsa, An Ji Dalili

Makinde: Gwamna Zai Mika Ragamar Mulki ga Mataimakinsa, An Ji Dalili

  • Ragamar jagorancin jihar Oyo za ta sauya daga hannun Gwamna Gwamna Seyi Makinde zuwa ga mataimakinsa, Bayo Lawal
  • Seyi Makinde ya rubuta wasika zuwa ga majalisar dokoki domin sanar da ita shirinsa na ganin Bayo Lawal ya ci gaba da jagorancin jihar
  • Rubuta wasikar zuwa ga majalisar na daga cikin tanadin da wani sashen kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi, idan irin wannan bukatar ta taso

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, zai fara hutun wata guda daga ranar Juma’a, 29 ga watan Agusta, 2025.

Gwamna Seyi Makinde zai mika ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa, Bayo Lawal, har na tsawon lokacin da zai kwashe yana hutu.

Gwamna Makinde na Oyo zai tafi hutu
Hoton Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, a wajen wani taro Hoto: @seyimakinde
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta kawo rahoto cewa hakan na kunshe ne a cikin wata wasikar da aka aika wa majalisar dokokin jihar.

Kara karanta wannan

Duk da ya yi murabus, an dakatar da tsohon shugaban majalisar dokokin Benue

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Makinde ya mika bukata gaban majalisa

An dai karanta wasikar ne yayin zaman majalisar na ranar Talata, 26 ga watan Agustan 2025.

A cewar wasikar da shugaban majalisar, Adebo Ogundoyin, ya karanta, an yi hakan ne bisa tanadin sashe na 190(1) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya.

Sashen dai ya wajabta wa gwamna ya tura rubutacciyar wasika ga majalisa kafin ya tafi hutu.

A cikin wasikar, Makinde ya bayyana bukatarsa ta tafiya hutu tare da mika ragamar mulki ga mataimakinsa, Bayo Lawal, wanda zai rike matsayin mukaddashin gwamna a duk tsawon lokacin hutun.

"Ina sanar da cewa a lokacin da aka ambata a sama, mataimakin gwamna, Bayo Lawal, zai rike matsayin mukaddashin gwamna. Zan koma bakin aiki a ranar Litinin, 29 ga watan Satumba, 2025 bayan dawowa daga hutu."

- Gwamna Seyi Makinde

Bukatar Makinde ta samu karbuwa a majalisa

Majalisar ta amince da wasikar tare da tabbatar da goyon bayanta domin samun saukin mika ragamar mulki ba tare da tangarda ba a lokacin da gwamnan ya tafi hutu, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Kara karanta wannan

PDP ta koka, ta zargi EFCC da garkame manyan 'ya 'yanta 2 a Kaduna

Gwamna Makinde zai tafi hutun wata 1
Hoton gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde Hoto: @seyimakinde
Source: Facebook

Shugaban majalisar ya sake tabbatar da cewa majalisar za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka kan doka don dorewar mulki a jihar.

Da wannan wasikar daga gwamnan da kuma amincewar majalisa, ana sa ran Bayo Lawal zai dauki nauyin cikakken jagoranci daga ranar 29 ga Agusta zuwa ranar 29 ga watan Satumba, 2025, lokacin da Gwamna Makinde zai dawo bakin aiki.

Majalisar dokokin ta jihar Oyo za ta dawo zaman ta na gaba a ranar 16 ga watan Satumba, 2025.

Makinde ya magantu kan ficewar Atiku daga PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi martani kan ficewar tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Atiku Abubakar, daga jam'iyyar PDP.

Seyi Makinde ya bayyana cewa ficewa Atiku Abubakar wata hanya ce ta cewa jam'iyyar daga rigingimun cikin gida da suka dade suna addabar ta.

Gwamnan na jihar Oyo ya yi ikirarin cewa, PDP ba za ta rage karfi ba ko rage wata dama da take da ita, saboda ficewar tsohon mataimakin shugaban kasan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng