Gwamna Ya Rusa Masallatai 40, Ƴan Arewa Sun Yi Asarar Biliyoyi a Kasuwar Legas
- Gwamnatin jihar Legas ta rusa fiye da masallatai 40 da shaguna 3,000 na 'yan Arewa da ke kasuwanci a kasuwar Alaba Rago
- Wazirin sarkin kasuwar Alaba Rago, Alhaji Adamu Katagum ya ce gwamnati ta rusa kasuwar da suka shafe shekaru 45 suna ginawa
- Wani dan kasuwa, Alhaji Muhammed Rabiu ya ba da labarin yadda jami'an tsaro suka rusa kasuwar, suka raba su da dukiyarsu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Lagos – Dubban ’yan Arewa masu kasuwanci a shahararriyar Kasuwar Alaba Rago sun nemi gwamnatin Jihar Legas ta biya su diyya.
'Yan kasuwar sun bukaci diyyar ne bayan asarar da suka ce sun tafka da tahaura ta Naira biliyan 20 sakamakon rushe kasuwar Alaba Rago da aka yi.

Source: UGC
Gwamnatin Legas ta rusa kasuwar Alaba Rogo
Kasuwar Alaba Rago, wacce aka kafa a 1979, ta shahara da harkokin kasuwancin kayan abinci, dabbobi, karafa da sauran kayan masarufi, inji rahoton Aminiya.
Hukumomin Jihar Legas sun sake rusa wasu sassa na Kasuwar Alaba Rago, wacce aka kafa tun 1979 da Hausawa suka mamaye da kasuwancin kayan abinci, dabbobi, karafa da sauran kayayyaki.
Tun a watan Mayu 2024, jami’an ’yan sanda suka shiga kasuwar da nufin kawar da baragurbi, kafin kuma sabon rusau ya biyo baya a ranar Lahadi, 17 ga watan Agusta.
Wannan rusau ya ci gaba har zuwa Laraba, 20 ga watan Agusta, lamarin da ya bar dubban ’yan kasuwa cikin rudani da rashin matsugunni.
"Muna biyan haraji" - Wazirin Alaba Rago
A cewar Alhaji Adamu Katagum, Wazirin Sarkin Alaba Rago, wannan rusau ya shafi rayuwar dubban iyalai da suke ci daga kasuwar.
Alhaji Adamu Katagum ya ce:
“Tun kafin wannan wuri ya bunkasa, ’yan Arewa ne suka zuba jarinsu wajen gyara shi, tun lokacin yana kurmi da fadama. Tsawon shekaru muna biyan haraji amma gwamnati ta rusa abin da muka gina da zufa, kudi da karfinmu.”

Kara karanta wannan
Jima: An tunawa gwamnoni 19 hanyar da za su samu 'makudan kudi' a Arewacin Najeirya
Wazirin Sarkin Alaba Rago ya kara da cewa an dauki lokaci mai tsawo wajen kafa kasuwar, amma a rana guda an rusa komai ba tare da an samar da mafita ga 'yan kasuwar ba.
Ya ce asarar da suka tafka ta haura Naira biliyan 20 bayan an rusa masallatai sama da 40 da shaguna kimanin 3,000 a kasuwar wadda suka kafa shekara 45 da suka gabata.

Source: UGC
'Rusa kasuwar ta rusa rayuwarmu' - 'Yan Arewa
Wani dan kasuwa, Alhaji Muhammed Rabiu ’Yan Masara, ya bayyana takaicinsa, yana mai cewa abin da ya faru ya sabawa adalci, musamman ganin irin rawar da al'ummar Hausawa ke takawa wajen bunkasa tattalin arzikin Legas.
Alhaji Muhammed ya ce:
“Tun daga 1999 muna mara wa jam’iyya mai mulki baya, amma sakamakon da aka ba mu kenan.”
'Dan kasuwar ya yi karin haske cewa duk kadarorinsu suna da takardu na doka, kuma ba su kafa shagunansu bisa sabawa ƙa’ida ba.
“Duk da haka, mun tashi ne a safiyar ranar Litinin, sai muka yi taho-mu-gama da ’yan sanda dauke da makamai, wadanda suka yi rakiya ga wadanda suka rusa mana dukiyoyinmu da rayuwarmu suka ruguje su cikin kiftawa da Bisimillah."
- Alhaji Muhammed Rabiu ’Yan Masara.
Har yanzu gwamnatin Jihar Legas ba ta fitar da wata sanarwa kan dalilan da suka haddasa rushe-rushen ba, lamarin da ya bar dubban ’yan kasuwa cikin rudani da fargaba.
Kwankwaso ya ziyarci 'yan kasuwar Alaba Rago
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya gana da shugabannin ’yan Arewa a Legas bayan rusa kasuwar Alaba Rago.
A yayin taron, Kwankwaso ya ce yana sane da irin matsalolin da Hausawa ke fuskanta a Legas, kuma ya jaddada cewa zai yi iya ƙoƙarinsa wajen ganin an samu sauƙi.
Hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya sanar da cewa tattaunawar ta mayar da hankali kan gano matsalolin da suka taso da kuma neman hanyoyin magance su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

