Bikin Wan Shagali: Jikar Marigayi Shugaba Buhari Za Ta Yi Aure
- Za a daura auren daya daga cikin jikokin tsohon shugaban kasan Najeriya, marigayi Muhammadu Buhari
- Jikar ta marigayi Buhari mai suna, Halima Amirah Junaid, ta kasance a karkashin kulawar Aisha Buhari bayan rasuwar mahaifiyarta
- Za a gudanar da daurin auren na ta ne a jihar Kaduna a cikin wannan watan da muke ciki na Agusta, inda tuni aka fara shirye-shirye shan biki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Halima Amirah Junaid, jikar tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari, za ta yi aure.
Halima Amirah Junaid na shirin yin aure da Walid Shehu Mu’azu a wani biki da za a gudanar a jihar Kaduna.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta ce shirye-shiryen bikin sun fara ne a makon nan a Abuja, inda tsohuwar uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta shirya wani taro na mata a matsayin wani ɓangare na shirin babban bikin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wacece jikar Buhari da za ta yi aure
Halima ’ya ce ga marigayiya Zulaihat Junaid, ɗiyar fari ta Buhari, wadda ta rasu a lokacin haihuwa.
Zulaihat ta yi aure da Junaid Abdullahi. Ita kuma ’ya ce ga Safinatu, matar farko ta Buhari, wadda ita ma ta rasu a shekarun baya.
Safinatu Buhari ta haifi yara biyar tare da Buhari, amma biyu daga cikinsu sun rasu sakamakon kamuwa da cutar sikila.
Abubakar Adamu, wanda shi ne mai kula da shirye-shiryen bikin, ya fayyace asalin dangin amaryar.
Ya tabbatar da cewa bayan rasuwar Zulaihat, tsohuwar uwargidan ƙasa, Aisha Buhari, ce ta ɗauki nauyin kula da jikokin na marigayi shugaban kasan.
Ba matar Malami ta haifi amaryar ba
Abubakar Adamu ya kuma karyata rahotannin da ake yadawa da ke ɗaukar Halima a matsayin ’ya ta ɗiyar Buhari da ta yi aure da tsohon babban lauyan tarayya kuma ministan shari'a, Abubakar Malami.

Kara karanta wannan
Jima: An tunawa gwamnoni 19 hanyar da za su samu 'makudan kudi' a Arewacin Najeirya
“Mahaifiyar amaryar ta rasu. Tana tare da mijinta lokacin da ta rasu. ’Yar uwarta ce ta auri Abubakar Malami. Har ma ɗan da aka haifa lokacin haihuwarta yana nan da rai. Ita ta rasu ne a lokacin haihuwa."
“Yaron yana nan da rai. Dukkan yaran suna tare da Aisha a Abuja, ita ce ke kula da dukkan al’amuran uwa. Amma babban bikin auren zai gudana ne ranar 30 ga watan nan."
"Al’adar ita ce mahaifi ne ke ba da auren ’yarsa."
- Abubakar Adamu

Source: Facebook
An shirya gudanar da daurin aure tsakanin Halima Amirah Junaid da Walid Shehu Mu’azu a ranar 30 ga watan Agusta a kihar Kaduna.
Bikin walima kuma zai gudana a shahararren wurin Kaduna Polo Club.
Obasanjo ya soki gwamnatin Buhari
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi kalamai masu kaushi kan gwamnatin marigayi, Muhmmadu Buhari.
Obasanjo ya bayyana gwamnatin tsohon shugaban kasan na Najeriya ta tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023, a matsayin gwamnatin farar hula mafi muni a tarihi.
Hakazalika, Obasanjo ya bayyana cewa Buhari ya gaza ta fannoni da dama wajen kawo sauye-sauyen da ya zargi magabantansa da kasa aiwatarwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
