Kyawawan hotunan auren Zahra Buhari da Ahmed Indimi na a

Kyawawan hotunan auren Zahra Buhari da Ahmed Indimi na a

Badai wani sabon labari bane dangane da aure Zahra, wato daya daga cikin yaran shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Ahmed wato yaron mai kudin gasken nan Muhammed Indimi.

Auren dai da aka bayyana cewar an daga shi sakamakon rahoton sirrin karkashin kasa da kafaffan yada labarai suka bayyana dangane da kayan lefen da akayima Amaryar. Sai gashi kuma an bayyana cewar 16 ga watan Disamban nan ne daurin auren.

Sai kuma gashi, hotunan ma'auratan da suka dauka domin auren nasu sun watsu a yanar gizo. Zahrah dai ta sanya kaya bakake inda ta daura bakin dan kwali a kanta wanda tayi kyau sosai, a inda angon nata ya sanya babban riga kalar ruwan toka da kuma hula baki.

Kyawawan hotunan auren Zahra Buhari da Ahmed Indimi na a

KU KARANTA: Dasukigate: Obanikoro ya sake kiran ruwa 

A ranar juma'a ne 18 ga watan Nuwamba dangin Zahra suka amshi kayan lefe a Aso Villa dake Abuja daga dangin Ahmed Indimi, inda suka hada akwatuna na musamman da aka kera kirar kamfanin LV. Akwatunan dai ana kiransu laife a al'adar hausawa, inda miji zai siyamma matar sa, kuma ya kai kafin ranar aure.

Akwatunan dai an cikasu ne da gwalagwalai da kuma damon na kwalliya da kuma tsadaddun atamfuna da takalma da kananan riga da kuma wando da turaruka da leshi da kuma kayan ciki dana bacci da dai sauran su.

Haka kuma a jikin akwatunan kirar LV din, an rubuta sunan Zahra, inda aka sanya ZBI wato (Zahra Buhari Indimi).

Muna tayasu murnan auren nan da zasuyi!

Ku biyomu a shafinmu na tuwita. @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: